A cikin wannan satin ne gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta bayyana sababbin shugabannin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, kwanaki kadan bayan kwamishinan matasa da wasanni, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya soke tsohon shugabancin kungiyar karkashin shugabancin Babangida Little saboda wasu dalilai.
Sai dai masoya kungiyar ta Pillars, wadda ake kira “MASU GIDA” sun ji dadin matakin da gwamnatin ta dauka na rushe wancan jagorancin sakamakon rashin tabuka abin arziki a kakar da aka kammala, inda kungiyar ta kare a mataki na 11 da kuma daukar sabon mai koyarwa, Paul Offor, wanda magoya bayan kungiyar suke ganin bai cancanta ba.
- Wakilin CMG Ya Zanta Da Shugaban Kasar Timor-Leste
- Kudurin Jam’iyyar Kwaminis Ta Kasar Sin Ya Shafi Manyan Tsare-Tsare Tare Da Matakai Na Zahiri
Sababbin shugabannin kungiyar, karkashin shugabancin Aliyu Nayara Mai Samba, da mambobinsa da suka hada da Salisu Muhammad Kosawa da Yusuf Danladi Andy Cole da Muhammad Usman da Ahmad Musbahu da Umar Umar Dankura da Rabiu Abdullahi da Nasiru Bello da Muhammad Danjuma Gwarzo da Mustapha Usman Darma da Muhammad Ibrahim (Hassan West) da Injiya Usman K/Naisa su ne za su jagoranci kungiyar sai kuma Abubakar Isa Dandago.
Jami’in yada labarai da kuma Ismail Abba Tangalash, a matsayin mataimakin Jami’in yada labarai.
Wadanne kalubale ne a gaban sababbin shugabannin?
Sabon mai koyarwa
A daren ranar Talata ne sabon shugabancin na Kano Pillars ya tabbatar da korar kociyan kungiyar, Paul Offor, wanda tsohon shugabancin kungiyar ya dauka kwanakin baya, wanda kuma wasu rahotanni sun nuna cewa wannan dalilin na daukar kocin yana daya daga cikin dalilan korar tsohon shugabancin.
Yanzu abin da yake gaban shugabancin kungiyar shi ne tabbatar da ganin an dauki sabon mai koyarwar da zai kawo canji sannan kuma wanda ya cancanta saboda Kano Pillars daya ce daga cikin manyan kungiyoyi a kasar nan, sabode haka suna bukatar kwaarrren mai koyarwa.
Gyara Halayyar Magoya Baya
Wasu suna ganin halayyar magoya bayan kungiyar tana daya daga cikin dalilan da suke sanyawa kungiyar take tsintar kanta a wani halin na rashin kokari saboda rashin hakuri da kuma daukar mataki na jifa ga alkalan wasa da abokan karawa da magoya bayan kungiyar suke yi.
A lokuta da dama an ga yadda kwamitin ladaftarwa na hukumar da ke kula da gasar firimiya ta kasa ke dakatar da magoya baya shiga Kallon wasa ko dauke Kano Pillars din daga Jihar Kano zuwa wata jihar ko kwashe mata maki saboda halayyar magoya baya kuma hakan babbar barazana ce ga kokarin kungiyar.
Sabon shugabancin kungiyar yana bukatar bita domin a nusar da su hakkin magoya baya da kuma rawar da za su iya takawa wajen ganin kungiyar ta samu ci gaba ta hanyar goyon bayan kungiyar ta hanyar da ta da ce.
Sannan akwai bukatar a fitar da wani tsari ga magoya baya wanda wannan alhakin shugabancin magoya bayan kungiyar ne, idan aka samu tsari mai kyau magoya baya kadai za su dinga samar da kudin shiga wanda za a dinga anfani da shi wajen toshe wata matsalar ta kudi.
Gyara Yadda Ake Daukar ‘Yan Wasa
Abu ne sananne a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, salon yadda ake daukar ‘yan wasa a kungiyar yana bukatar gyara da kuma sanya ido tare da nuna kwarewa. Kamar yadda rahotanni suka bayyana, da yawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar da suka buga kakar wasan da ta gabata sun tafi, sun koma wasu daga cikin abokan hamayyar Kano Pillars wanda hakan yana nufin akwai bukatar a kawo wasu domin cike gurbinsu.
Sai dai ba kawai kawo wasu ‘yan wasan ba ne mafita, akwai bukatar yin tsari wajen daukar ‘yan wasan kamar yadda yake a tsare kuma zai kasance kungiyar za ta samu riba idan har an tashi sayar da dan wasa zuwa wata kungiyar a nan gida Nigeria ko kuma kasashen waje.
Tsarin daukar dan wasa ta hannun wakilinsa, wato (Agent) a turance yana da illa sosai domin dan wasa yana iya barin kungiya a duk lokacin da ya ga wata dama ta zo masa saboda ba kwantiragi aka shiga da shi ba kamar
yadda yake a tsare.
Da yawa daga cikin wakilan ‘yan wasa sun yi amfani da Kano Pillars wajen tallata ‘yan wasansu a gasar firimiya da ma kasashen waje kuma idan dama ta samu sai su dauke ‘yan wasan su tafi tun da babu wata yarjejeniya da aka kulla ta adadin wasu shekaru ko watanni.
Aikin da yake gaban sabon shugabancin Kano Pillars a yanzu a kan maganar daukar sababbin ‘yan wasa shi ne dole ne a kaucewa hanyar dodorido da yin ungulu da kan zabo ga kungiyar domin samun ci gaban da ake abukata.
Biyan ‘yan wasa hakkokinsu
Hakkokin ‘yan wasa su ne muhimman abubuwan da shugabancin ya kamata ya kalla, domin biyan dan wasa albashi da ragowar hakkokinsa yana daya daga cikin abubuwan da suke karawa ‘yan wasa kwarin gwiwa domin su dage su yi abin da ya kamata.
Sai dai tuni gwamnatin Kano ta yi alkawarin biyan ‘yan wasan hakkokinsu wanda hakan yake nufin nan gaba kadan abubuwa za su gyaru a kungiyar.
Hanyoyin Samun Kudin Shiga
Kano Pillars kungiya ce da ta karkashin gwamnatin jiha kuma ana biyansu albashi ne kamar yadda gwamnati take biyan albashi ga ma’aikatanta, kasancewar wasan kwallon kafa yana da farin jini da kuma kasancewar kungiyar a Jihar Kano take, akwai bukatar sabon shugabancin ya samar da wani tsari wanda zai kawo hanyoyin shigowar kudi kungiyar ta hanyar neman kwararru su samar da yanayin da za a samu kudin shiga da
kuma kafa kwamiti mai karfi wajen neman talla ta hanyar tuntubar ‘yan kasuwa da kamfanoni.
Yada labarai
Wannan shi ne bangaren da za a iya cewa tuni ya fara aiki kai tsaye kuma aka fara gani da ido daga fara aikin sabon shugabancin kungiyar, duk da cewa ba abin mamaki bane kasancewar wadanda suke da alhakin wannan fanni na yada labarai daman kwararru ne a bangaren.
Abubakar Isa Dandago da Isma’il Abba Tangalashi sun yi suna wajen bayar da labaran wasanni, sannan ba iya bayar da labarin ba, salon bayar da labarin da kwarewar da suke da ita ce ya sa suka kasance cikin kunshin shugabancin Kano Pillars. Tuni bangaren yada labarai ya fara aikinsa ta hanyar fitar da sanarwa irin yadda manyan kungiyoyi suke yi tare kuma da bude shafukan sada zumunta domin isar da sako da magoya bayan kungiyar kai tsaye, hakan kuma zai taimaka wajen wayar da kan magoya baya a nan gaba domin ta kafar yada labarai ne kawai magoya baya za su dinga sanin halin da kungiyar take ciki da kuma rawar da suma za su dinga takawa wajen ba wa kungiyar goyon baya a tsare ba tare da kaucewa doka ba.
Tuni dai aka fara ganin canji a fannin yada labarai kuma hakan yana nufin nan gaba kadan kungiyar za ta fara samun kudin shiga ta hanyar shafukan sada zumunta. Idan har bangaren yada labarai za su dage wajen samar da labarai na hoto da bidiyo da sauran hanyoyin yadda manyan kungiyoyi na duniya suke yi na mayar da hankali a kan kafofin yada labarai na zamani ana sakawa a shafukan sada zumuntar kungiyar hakan zai kawo canji sosai kuma za a tabbatar da cewa an saka kwarya a gurbinta.