A Jamhuriyar Nijar, an ƙaddamar da sabon tsarin riƙon ƙwarya na shekaru biyar ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahman Tiani a yau Laraba.
A yayin bikin, an ɗaukaka muƙamin Tiani daga Burgediya Janar zuwa Janar mai taurari biyar, sannan aka ayyana shi a matsayin Shugaban Jamhuriyar Nijar da Babban Kwamandan Askarawan ƙasar.
- Yadda Binciken Kayan Tarihi Ke Zakulo Asalin Magabata Da Wayewar Kansu A Kasar Sin
- Majalisa Ta Yi Watsi Da Kara Akan Akpabio Kan Zargin Neman Yin Lalata Da Natasha
Bayan ƙaddamar da shi, Tiani ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki, ciki har da rushe dukkannin jam’iyyun siyasa sama da 170 da kuma bayar da umarnin sakin wasu fursunonin siyasa da na fararen hula da aka daɗe ana tsare da su.
Wannan mataki ya biyo bayan shawarar da aka cimma a taron da aka gudanar tsakanin 15 zuwa 20 ga watan Fabrairu, inda aka yanke hukuncin bai wa gwamnatin riƙon ƙwarya tsawon shekaru biyar kafin miƙa mulki.
Wannan na nufin daga yau, 26 ga watan Maris 2025, Janar Tiani zai ci gaba da shugabancin Nijar na tsawon shekaru biyar, bayan watanni 19 da ya shafe a mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp