Jaridar ‘Business Day’ ta karrama Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, da lambar yabo na gwamna Mafi kwazo a fagen yi wa al’ummar jiharsa hidima.
An gudanar da taron Bada lambar yabon gwarazan na shekarar 2022 ne a ranar Alhamis a Abuja Continental Hotel (Sheraton Hotel and Towers) yayin da mataimakin Gwamnan, Dr. Manassah Daniel Jatau ne ya karɓi kyaututtukan a madadinsa.
Sauran fitattun mutanen da suka samu lambar yabo a bikin sun hada da Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki, da Ministan Kwadago da Tallafi Chris Ngige, da Babban Daraktan Hukumar Bunmasa Fasahar Sadarwa ta Kasa NITDA, Kashifu Inuwa da dai sauransu.
Mawallafi kuma shugaban kamfanin ‘Business Day Media’, Mr Frank Aigbogun, ya ce an shirya taron ne don karfafa gwiwar shugabanni a matakin jihohi su rungumi al’adar aiki tukuru, da samar da ribar demokradiyya ga al’umma.
A cewarsa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya fafata ne da wasu gwamnoni a bangarori daban-daban, kuma jihar sa ta zama zakara wacce tafi kowace jiha a fagen saukaka harkokin kasuwanci, kuma jihar da ta fi inganta yankunan karkara da birane.
“An cimma hakan ne bayan da kwamitin bada lambar yabon wanda ya kunshi fitattun mutane ya tattara bayanan da suka dace kai tsaye, da kuma nazarin sauran bayanan da aka tattara daga ɓangarori daban-daban na tattalin arziki da zamantakewa.
“Mun ga ci gaba sosai a Jihar Gombe tun bayan hawan Gwamna Inuwa Yahaya, mun ji irin nasarorin da ya samu a fannin kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa, da raya karkara da zuba jari. A ‘yan kwanaki kadan da suka gabata mun ga yadda jihar sa ta samu matsayi na daya a fagen saukala harkokin da harkokin kasuwanci.
“Hakan bai zo mana da mamaki ba ganin yadda gwamnan yake ta lashe lambobin yabon da mukan bayar a kai a kai bayan shirya gasa, muna taya mai girma gwamna murna kuma muna kara masa kwarin guiwa kan ya ci gaba da irin wannan kokari nasa”.
Da yake karbar lambar yabon a madadin Gwamna Inuwa, Mataimakin nasa Dakta Manassah Daniel Jatau, ya bayyana karramawar a matsayin kalubalen da zai zaburar da shi wajen kara jajircewa kan aikin da ya saba.
Sai ya yaba wa kafar yada labaran bisa wannar karramawa ta aiki tukuru da nagarta a harkokin mulki.
“Zan fara da yaba wa Mawallafin wannar jarida ta Business Day bisa wannan karramawa da lambar yabo. Wannan wani aiki ne mai matukar muhimmanci da kuka yi. A makon daya gabatan nan muka samu lambar yabo a matsayin jiha mafi fice a fagen saukaka kasuwanci da kuma wani a matsayin gwamnati mafi haba-haba da ma’aikata, daga kungiyar Kwadago ta kasa TUC, kuma a yau ma ga shi muna sake samun wata lambar yabon na gwamnati mafi kwazo a fagen yiwa al’ummar ta hidima”.
“A gare mu, samun lambar yabo wani kalubale ne, nauyi ne da kuma tsammanin cewa za mu yi fiye da haka. Bisa tsari na fahimta, babu wanda zai iya yin komai shi kadai. Muna godiya da gudunmawar da kowa ke bayarwa a Jihar Gombe, musamman wadanda suka bada gudunmawa wajen samun wannar lambar yabo. Don haka mun sadaukar da wannar lambar yabo ga dokacin al’ummar jihar bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar gwamnatin mu”.
“Ina gayyatar ku zuwa Jihar Gombe don ku ganewa idon ku cibiyar masana’antu ta Muhammadu Buhari mai girman kadada 1000, inda muka samar da duk abin da ake bukata da suka hada da wutar lantarki daga madatsar ruwa ta Dadinkowa, da ayyukan more rayuwa na zamani da abubuwan jin dadin jama’a da kuma zaman lafiya domin kasuwanci ya bunkasa. Ina kuma gayyatar ku da ku zo ku zuba jari a Jihar Gombe, muna da kyakkyawan yanayi na kasuwanci”.