Abdulrazak Yahuza Jere" />

Jaridar People’s Daily Ta Wallafa Rahotanni Kan Bukukuwan Murnar Shiga Sabuwar Shekara Na CCTB

A kwanakin baya ne, jaridar People’s Daily ta kasar Sin ta ruwaito rahotanni da dama game da bikin kade-kade da raye-raye na shekara ta 2019 da gidan talabijin na CCTB zai gabatar, don murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara ke nan.
Rahotannin sun ce, a matsayin bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin na farko da za’a yi tun bayan da aka kafa babban gidan talabijin da rediyo na kasar wato CMG a takaice, bikin na bana, mai taken “Yin kokari a sabon zamanin da muke ciki, da murnar sabuwar shekara mai alheri”, zai maida hankali sosai don kayatar da ‘yan kasar Sin masu kallo a duk fadin duniya.
Ha wa yau, za’a gabatar da bikin ta hanyoyin sadarwar zamani daban-daban. Kuma yayin da suke kallon bikin ta wayar salula kuma, masu kallo za su iya mika sakwannin gaisuwarsu ta kafofin kamfanonin Baidu da Douyin.
A cikin rahoton da jaridar People’s Daily ta ruwaito a ranar 29 ga wata, an kuma ce, za’a yi amfani da fasahar sadarwar zamani ta 5G don gabatar da bikin na bana, al’amarin da ya kasance wani babban ci gaba da CMG ya samu wajen raya hanyoyin sadarwar zamani na fasahar 5G. Hakan na nuna cewa, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya zama sabuwar muhimmiyar kafar yada labarai wadda ke watsa labarai da rahotanni ta sabbin hanyoyin sadarwar zamani a duk duniya.(Murtala Zhang)

Exit mobile version