A yau Talata ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi tsokaci kan bikin cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Amurka.
Kakakin ya ce, shekarar 2024, shekara ce ta cika shekaru 45 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka, lamarin da ya yi babban tasiri a tarihin Sin da Amurka da ma huldar kasa da kasa. A cikin shekaru 45 da suka wuce, dangantakar Sin da Amurka ta fuskanci kalubaloli da dama kuma ta jure.
- Mutane Kimanin Miliyan 135 Sun Yi Yawon Shakatawa A Yayin Hutun Bikin Sabuwar Shekara A Sin
- Sin Ta Kaddamar Da Kidaya Ta Kasa A Fannin Tattalin Arziki
Kakakin ya kara da cewa, darajar cinikayya tsakanin kasashen biyu ta haura daga kasa da dalar Amurka biliyan 2.5 a shekarar 1979 zuwa kusan dala biliyan 760 a shekarar 2022. Kana, yawan jarin da kasashen biyu suka zuba wa juna ya karu daga kusan sifili zuwa sama da dala biliyan 260, kuma an kulla huldar abokantaka tsakanin larduna, jihohi da birane guda 284 a kasashen 2. Kazalika, kasashen biyu sun gudanar da hadin gwiwa a fannoni daban daban na kasa da kasa da na shiyya-shiyya da kuma batutuwan da suka shafi duniya baki daya. Tarihi ya nuna cewa, bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka ba kawai tana taimaka wa al’ummomin kasashen biyu ba, har ma ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban duniya.
Kakakin ya ci gaba da cewa, a taron kolin da aka yi a birnin San Francisco, shugaba Xi Jinping da shugaba Joe Biden sun cimma matsaya sama da 20 a fannonin siyasa da harkokin waje da cinikayya da harkokin kudi, da musayar al’umma, da tafiyar da harkokin duniya, da harkokin soja da tsaro.
Kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Amurka wajen aiwatar da muhimman fahimtar juna da sakamakon da aka cimma a taron kolin, tare da raya fahimtar juna, da sarrafa sabani yadda ya kamata, da ciyar da hadin gwiwar moriyar juna gaba, da sauke nauyi a matsayin manyan kasashe, da sa kaimi ga mu’amala tsakanin juna ta yadda za a tafiyar da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu a kan turba mafi dacewa don amfanar kasashen biyu da ma duniya baki daya, a cewar kakakin. (Yahaya)