Jawabin Xi Ya Saitawa Yankin Asiya Da Fasifik Alkiblar Cin Galaba Kan Annobar COVID-19 Da Farfadowar Tattalin Arziki

Daga CRI Hausa,

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jerin shawarwari game da zurfafa hadin gwiwa da hanyar da yankin Asiya da Fasifik zai bi, wajen cin galaba kan annobar COVID-19 da farfado da tattalin arziki.

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ne ya bayyana haka jiya, lokacin da yake amsa tambayoyi game da halartar taro na 28 na shugabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin Asiya da Fasifik na APEC da shugaban kasar Sin ya yi a jiyan.

Da yake bada misali da jawabin na shugaba Xi kan daukaka bude yankin, Wang Yi ya ce, wannan na nuna buri na bai daya na al’ummar yankin, ta fuskar neman hadin kai da zaman lafiya, tare da saita alkiblar hadin gwiwar yankin Asiya da Fasifik, wanda ba makawa zai samu goyon baya daga karin kasashen yankin da ma na duniya baki daya.

Har ila yau, Wang Yi ya ce, Sin za ta ci gaba da kasancewa mai goyon baya da inganta hadin gwiwar tattalin arzkin yankin Asiya da Fasifik, da hada ci gabanta da na yankin, da ingiza bude kofar yankin ta hanyar bude kofarta da inganta raya tattain arziki da ci gaban al’umma da kyautata rayuwarsu. (Fa’iza Mustapha daga sashen Hausa na CRI)

Exit mobile version