Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya bayyana wasu hanyoyin tsaftace zaben NMijeriya cikin sauki.
Jega ya bayyana hanyoyin ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wurin wani taron kwanaki biyu da ya gudana a Jihar Akwa Ibom.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Karbo Bashin Dala Biliyan 3.45 Daga Bankin Duniya
- Shin Wasan Kwaikwayon Na Zaben Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Ta Kawo Karshe Ne?Â
Ya ce matukar ana bukatar a tsaftace zaben Nijeriya, to dole ne ya kasance ba shugaban kasa ba ne yake nada shugabannin hukumar INEC.
Tsohon shugaban INEC ya yi kira da a yi wa dokar zabe na 2022 garanbawul.
A cewarsa, duk da cewa dokokin zaben Nijeriya na yanzu za a iya cewa su ne mafi kyau a tarihin kasar nan, amma ba su zama cikakku ba, akwai bukatar a kara yin wasu gyare-gyare domin kawar da rudani da fayyafe abubu yadda suke da kuma karfafa wasu bangarorin dokokin.
Ya ce gyare-gyaren su kasance sun tilasta saka sakamakon zabe ta na’ura a zabe mai zuwa na 2027.
Game da shugabancin hukumar INEC, Jega ya jadda cewa kamata ya yi a cire hannun shugaban kasa wajen ikon nada shugaban INEC da kwamishinonin zabe, domin a ceto hukumar daga nuna bangaranci ko bambanci ko kuma taimaka wa wasu.
Ya kara da cewa ya kamata a sake duba dokokin zabe domin tabbatar da cewa an warware duk matsalolin da suka taso wajen gudanar da zabe da yanke hukunci kafin ranar rantsarwa.
Masu ruwa da tsaki da dama sun bayyana damuwarsu kan sashi na 64 na dokar zabe, wanda ya bayyana tsarin yadda za a bayyana sakamakon zabe, inda cikin sauki za a iya yin magudi da kuma kawo rudani.
Jega ya ce ya kamata a fayyace wannan sashe ta tilasta saka sakamakon zabe ta na’ura tun daga rumfunan zabe da har izuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe daban-daban a fadin kasar nan.
“INEC za ta sami isasshen lokacin da za ta shirya domin wannan lamari, idan an yi wa dokar kwaskwarima da wuri kafin zaben da ke tafe, in ji shi.
Haka kuma, Jega ya yi kira ko dai a bullo da wani tsari da zai bayar da damar fara yin zabe da wuri ga ma’aikatan INEC, masu sa ido da direbobinsu da ‘yan jarida, ko kuma wani tsari na musamman da zai ba su damar yin kada kuri’a a ranar zabe, musamman ma a lokacin zaben shugaban kasa.
Tsohon shugaban INEC ya bayar da shawarar barin ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje su kada kuri’unsu a kalla zaben shugaban kasa, domin ba su damar yin zabe, musamman wadanda suke aiki a kasashen ketare.
Ya ce akwai bukatar bai wa mata damar tsayawa takara a kowacce jam’iyya na kashi 35, tun daga mukamin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalsa, shugaban kananan hukumomi da kansiloli.
haka zalika, ya ce ya kamata a bai wa INEC ikon gudanar da zaben cike gibi da zarar an samu hakan.
A halin da ake ciki kuma, Farfesa Attahiru Jega, ya musanta cewa an yi magudi a zaben 2023.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa Jega ya ce an yi magudi a zaben 2023, a wani taro na kwanaki biyu da majalisar dattawa ta shirya a Ikot Ipene na Jihar Akwa Ibom.
“Mun ga a zabukan 2023, illar kawai yadda masu rike da madafun ikon ke samun damar nada makusantarsu a cikin hukumar zabe domin su taimaka musu wajen lashe zabe,” in ji shi.
Sai dai a wata sanarwa da ta fito daga hannun babban mataimakinsa, Princess Hamman-Obels, Jega ya ce rahotannin da suka bayyana cewa ya ce an tafka magudi a zaben 2023 ba daidai ba ne kuma ba su dace da matsayinsa ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hankalin Farfesa Attahiru Jega ya karkata ne ga wani rahoto na yaudara da aka buga a jaridu da dama na intanet, inda ya ce an yi magudi a zaben 2023.
“Rahoton da aka yi ba daidai ba ne kuma ba dace da matsayin Farfesa Jega ba, lallai ya musanta yin wannan kalamai game da zaben 2023.”