Shugaban karamar hukumar Gwaram kuma sabon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi Nijeriya reshin Jihar Jigawa, Hon Abdurahman Salim Lawan Gwaram ya bayyana cewa Jigawa za ta samar da kashi 25 na shinkafar da Nijeriya ke bukata.
Ya ce Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Nnamdi Danmodi ya yi tsari ta yadda nan da dan lokaci kadan da ikon Allah Jigawa za ta noma shikafa kashi 25 cikin 100 na shinkafar da Nijeriya take bukata a duk shekara.
- Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Mutane 9 A Jigawa
- ‘Yansanda Sun Kama Matashi Kan Zargin Kashe Mahaifinsa Har Lahira A Jigawa
Hon Abdurahman ya bayyana hakan ne a lokacin yake ganawa da manema labarai.
Ya kara da cewa Gwamna Danmodi ya yi tsari na samar da tan 300 wanda kowanne mazabar dan majalisar jiha za ta samu tan goma, sai kuma kari da za a bai wa hamshakan manoma kari kan 300 na mazabu kananan hukumomin Jihar 27, ga shirin tallafa wa manyan manoma 1,000 da za su noma hekta 500 a Jihar ta Jigawa, akwai tsarin tallafa wa manoma 200 a kowacce karamar hukuma ta jihar ta hanyar ba su kayan aikin noma.
Har ila yau, Hon Abdurahman ya kara da cewa a kokarin gwamnan na sama wa matasa aikin yi, yanzu haka an horar da mata sama da dubu 100, dinkin hula na zamani da kuma tallafi da za a ba su da kayan aiki don bunkasa sana’o’insu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp