Mahukunta a shirin aikin noma da ke jure wa sauyin yanayi (ACReSAL), sun bayyana Jihar Bauchi a matsayi jihar da ta fi amfana da shirin a tsakanin jihohin kasar nan.
Bankin duniya ne ke tallafa wa shirin ta hanyar zuba miliyoyin daloli, don magance kalubalen sauyin yanayi da sauran kaluablen da ke yi wa fannin aikin noman tarnaki da samar da wadataccen abinci.
- Attajiri Abdul Samad Rabiu Zai Karbi Ribar Dala Miliyan 79.4 Daga Kamfaninsa Na Abinci
- Gwamnatin Tarayya Ta Umarci A Sayar Da Kamfanonin Samar Da Wuta 4
Dakta Ibrahim Kabir, Jami’in shirin na ‘ACReSAL’ ne ya bayyana hakan, a taron bayar da horo na kwana daya da aka shirya wa masu ruwa da tsaki a kan zaizayar kasa a jihar.
Har ila yau ya sanar da cewa, Gwamnan Jihar; Bala Abdulkadir Mohammed ne, gwamna daya tilo da ya nada babban mai bayar da shawara ta musamman a wannan shiri na ‘ACReSAL’.
Ya kara da cewa, ko shakka babu hakan ya nuna a zahiri irin muhimmancin da gwamnan ya bai wa wannan shiri na ‘ACReSAL’.
Kabir ya sanar da cewa, Jihar Bauchi na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar matsalar zaizayar kasa, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki da su taimaka, domin lalubo da mafita a kan wannan matsala, don amfanin daukacin al’umma baki-daya.
A cewarsa, tawagar ta ‘ACReSAL’; ta zo jihar ne don sake lalubo mafita a kan zaizayar kasa a fadin jihar baki-daya