Connect with us

RAHOTANNI

Jihar Kebbi Ta Kaddamar Da Feshin Maganin Kurona A Makarantun Sakandare 

Published

on

Gwamnan jihar Kebbi a jiya ta kaddamar da feshin Maganin cutar kurona a Makarantun Sakandare da kuma firamare na duk fadin kananan hukumomin 21 na  jihar.

Bayanin hakan ya biyo bayan ziyarar zagayen makarantun Sakandare na cikin Babban Birnin jihar da shugaban Kwamitin  korona, Alhaji Jafaru Muhammad  tare da mambobin Kwamitinsa  domin ganin irin yadda Shuwagabannin makarantun a jihar ke bin dokokin da hukumar NCDC ta sanya kafin bude makarantun a duk fadin kasar Nijeriya.

Inda shugaban kwamitin ya kaddamar da feshin Maganin Kurona da za a gudanar a dukkan makarantun sakandare da na firamare a kananan hukumomin 21 da ke ajihar ta kebbi.

Shugaban na kwamitin korona a jihar ya ce “Za mu tabbatar da mun kai ziyara a dukkan makarantun jihar Kebbi domin ganin cewar an bi dokokin tsarin hukumar NCDC don kauce wa barkewar cutar korona a makarantun, in ji shugaban kwamitin korona na jihar”.

Kwamitin dai ya samu ziyartar makarantun sakandare guda uku mallakin gwamnatin jihar Kebbi da kuma makarantun biyu masu zaman kansu a cikin jihar ta Kebbi.

Makarantun da kwamitin saka ziyarta sun hada da Makarantar Kimiya ta Nagari da ke a Birnin-Kebbi wato (Nagari Science College), makarantar ‘yan mata wato (Unity Gobernment Girls’ College Birnin-kebbi) . Sauran sun hada da Kebbi Capital College da kuma Royal Leads Academy dukkan su  na cikin Babban Birnin jihar ta Kebbi ne.

Haka kuma kwamitin korona na jihar sun bada kayan kariya ga kamuwa da cutar korona kamar handsernitizer, facemask da kuma na’urar gwaji zafin jiki a dukkan wadannan makarantun da kwamitin suka ziyarta.

Ya kuma kara da cewar “Sauran makarantun sakandare da na firamare dukkansu za su samu wadannan kayan, in ji shi”.

Daga nan ya ja kunnuwan shuwagabannin makarantun sakandare da su tabbatar da sun kiyaye dokokin da hukumar NCDC ta sanya. Ya kuma bukace su da su kafa kananan kwamiti a Makarantun su don kula da dokokin  korona.

Daga karshe ya yabawa shugabannin kan irin goyon bayan da suke bayar wa wurin ganin cewar ba a samu barkewar cutar korona ba.

 
Advertisement

labarai