Maryam Abdullahi daga Jihar Zamfara ta lashe gasar karatun Al-Qur’ani ta ƙasa karo na 14 ta Mata na makarantun sakandare marasa koyar da harshen Larabci a Nijeriya.
Gasar wacce ƙungiyar RIBADA te shiryawa tare da haɗin gwuiwar gwamnatin Jihar Katsina, inda ‘yan takara daga jihohi daban-daban suka fafata wajen haddace Hizifi 60, da 40, da 20, da 10, da kuma hizifi biyu.
- Ba Mu Da Hannu A Kisan Isma’il Haniyeh – Amurka
- Kasurgumin Dan Ta’adda Ya Mika Wuya Ga Sojoji A Borno
Maƙasudin Gasar
Sheikh Shu’aibu Shehu, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, ya bayyana cewa gasar na da nufin ƙarfafa haddar Al-Qur’ani da kuma nazarin sa tsakanin ‘yan mata a makarantun sakandare marasa koyar da harshen Larabci.
Ya kara da cewa gasar farko ta gudana ne a Kano a shekarar 2012, yayin da Katsina te zama jiha ta 14 da ta karɓi baƙuncin gasar.
Sheikh Shehu ya yi kira ga ɗalibai da su ci gaba da neman ilimi tare da bin koyarwar Al-Qur’ani.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Katsina, Hajiya Zainab Musawa, da Mataimakin Gwamnan Jihar, Malam Faruk Lawal-Jobe, sun yaba wa masu shirya gasar tare da tabbatar da goyon bayan su ga ilimin ‘yan mata.
Sauran waɗanda suka yi nasara daga rukunoni daban-daban na gasar su ne: Farida Zakariyya daga Jihar Kaduna ta lashe hizifi 40, da Aisha Sa’ad daga Katsina ta lashe hizifi 20, da Maimuna Adam-Jibril daga Borno ta lashe hizifi 10, yayin da Fatima Adam daga Jigawa ta lashe hizifi biyu.
Kyaututtukan da ka rabar sun haɗa da firiji, da Keken ɗinki, da barguna, da kayan sawa, da kuɗi.
Dr. Aliyu Abdullahi, Shugaban ƙungiyar na ƙasa, ya yi alkawarin ɗaukar nauyin wacce ta zo ta ɗaya zuwa Umrah.