A kasar nan ana yawan noman waken soyan saboda irin amfanin da yake da shi, musamman ganin cewa, ‘yan’adam da dabbobi na amfani da shi.
Har ila yau, a fadin duniya, ana gudanar da hada-hadar sa, inda kamfanonin da ke sarrafa amfani gona suke sayen da yawa domin sarrafa shi zuwa sauran nau’ukan abinci.
- Da Dumi-Dumi: Sarauniyar Ingila, Elizabeth Ta Rasu
- PDP Ta Koka Kan Yadda Jami’an CJTF Ke Cin Zarafin ‘Ya’Yanta A Borno
Bugu da kari, a kasar nan bukatarsa na kara karuwa a kullum musamman ganin cewa, ana yin amfani da shi wajen samar wa da yara kanana abincin gina jiki.
A daukacin fadin kasar nan, akwai jihin da suka yi fice wajen noman waken soya, jihohin su ne, Kaduna da Kebbi da Kwara da Jigawa da Katsina da kuma Borno.
Sauran jihohin sun hada da, Benuwai da Nasarawa da Kaduna da Kebbi da Kwara da Jigawa da Katsina da Borno da Kano da Zamfara da Gombe da kuma birnin tarayya Abuja da ma wasu sassan Kudu maso Yamma ke kan gaba wajen nomawa.
Manoma waken soya a kasar sun sanar da cewa, akwai matukar bukatar gwamnati, musamman ta taryya da ta ba su tallafi don su samu damar kara bunkasa noman waken soya kasar nan da kuma kara fitar da shi zuwa kasuwar duniya, inda hakan zai sa su samu damar kara samun riba.
Sai dai, sun nuna jin dadinsu akan yadda Babban Bankin Nijeriya CBN a karkashin shirin aikin noma na Anchor Borrowers suka samu tallafi daga gun gwamnatin tarayya, inda suka sanar da cewa, tallafin ya taimaka wa sana”‘ar su matuka tare da kuma kara samarwa da kansu kudaden shiga.
An ruwaito wasu manoman na waken soya sun shelanta cewa, za su noma tan da dama na waken soya, musamman don su kara samar da wadataccen sa a cikin kasar nan, ganin cewa, bukatar waken, musamman a kasar nan, na kara karuwa.
A cewar su, masana’antun da ke sarrafa waken na ci gaba da kara bukatar ta waken, inda suka bayyana cewa, a saboda haka, za su kara kaimi don noman waken na soya yadda zai wadaci masana’antun.
Sun yi nuni da cewa, har yanzu a fadin duniya, ana ci gaba da nuna bukatar ta waken soya, inda suka ce, amma sai idan sun wadata kasar nan da waken soyar ne, za su fara tunanin fitar da shi zuwa ketare.