Jinjina Ga Manufofin Nijeriyar Jiya

Nijeriyar Jiya

Ga mai bibiyar wannan rubutu, ya kwana da sanin cewa, a na yunkurin tattauna batutuwa ne game da irin yadda wasu kyawawan manufofin wannan Kasa ta Nijeriya suka kasance, cikin wasu Shekaru da su ka gabata. A fili yake cikin rubutun, a na son haskawa mai karatu ne cewa, cikin wadancan lokuta da suka shude na-dauri, a zahirance, Kasar ta fi hawa bisa saiti abin alfahari, idan aka dubi doron manufofinta da ta doru a kai, gami da aikata su a aikace, a fagen hulda da sauran Kasashen Duniya, sabanin irin yadda lamura su ka dawo su na tafiya daga bisani. Dan Nijeriya ya tambayi masana shari’a a wannan Kasa, za su tabbata masa da cewa, a rubuce a yau, Kasar Nijeriya, ta kasance guda daga cikin Kasashe a Duniya, wadda Kundin Tsarin Mulkinsu ya tsaru, ya yi matukar kyawo gwanin ban sha’awa a rubuce : to yaya batun shari’ar ke gudana kuma a aikace cikin sassan Kasar a yau?. Shi ya sanya wannan dandamali zai fi karkata ne ga aiki tsagwaro karara zahiran, wajen gabatar da abin tattaunawar, ba molanka ba.

Ko A Dauri An Soki Manufofin Nijeriyar

Na’am, yana da kyau mai karatu ya fahimta cewa, ba a nufin daukacin manufofin harkokin wajen Nijeriyar Jiya babu makusa ba ne, samsam, sai dai za mu karkatar da kalaman namu ne zuwa ga namijin kokarin gwamnatocin da suka gabatan, wajen dabbaka manufofinsu game da Kasashen wajen, ta fuskoki abin a yaba, sannan masu alfanu ga wannan Kasa ta Nijeriya, kuma masu tsantsar ma’ana ga nahiyar Afurka da ma wasu sassan Duniya na wancan lokaci.

Hatta manyan Kasashe irinsu Amurka, Faransa, Chana da sauran Kasashe da ke da karfin tattalin arzikin Kasa a yau ko a jiya, su na da irin nasu manufofin tafiyar da harkokin Kasashen ketare a bin kyama ko suka. Saboda haka, Nijeriya ba za ta zamto waren-gwanki ba, ta fuskacin zuwa da wasu manufofi da suka cancanci hantara ko kalubalanta.

Ko mai karatu bai san miyagun manufofin tattalin arziki hada da siyasa irin na wadancan manyan Kasashe ga sauran al’umar Duniya musamman mutanen Afurka, a jiyan da yau!. Ko mai karatu bai san manyan Kasashen, na tatsar tattalin arzikinsu ne daga raunanan Kasashe ne ba?, ko mai karatu bai san cewa manyan Kasashen, na taka mugunyar rawa a jiya da yau, wajen dankarawa al’umar Duniya musamman Kasashen Afurka, shugabannin da suke “yan korensu ne ba, don samun cigaba da rorar arzikin Kasa ta barauniyar hanya?, ko mai karatu bai sani ba cewa, irin wadancan manyan Kasashe, na da hannu dumu-dumu wajen haifar da mummunan yanayi na rashin tsaro a cikin irin Kasashenmu ne ba? Ko mai karatu bai san da hadin-bakin su waye aka kashe marigayi Janar Murtala Ramat Muhammad, da kuma marigayi Janar Sani Abacha ba? Ai da hadin-bakin irin wadancan manyan Kasashen ne! Saboda haka, don wasu masu sharhi sun ci gyara ko kalubalantar wasu daga manufofin kasashen ketare na gwamnatocin baya, musamman irin gwamnatin Balewa da Murtala da Gowon, ba wani sabon labari ba ne.

Wasu masu sharhi, na ganin wasu daga manufofin Kasashen ketare karkashin gwamnatin marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, na da wasu siffofi ne kamar haka;

-Gwamnati ce mai ra’ayin “yan mazanjiya.

-Gwamnati ce marar ra’ayin “yan sauyi.

-Gwamnati ce da ke sanda wajen tafiyar da manufofinta.

-Gwamnati ce da babu gamsarwa cikakkiya cikin kunshin manufofinta.

-Gwamnati ce da ba a dorawa daga inda aka tsaya. Sannan,

-Gwamnati ce da ke son nuna cewa tana da tarbiyya.

(Idang 1973; Alkali 2003; Jega and Farris 2010 : 4).

Akwai daga masu kalubale, wadanda ke fassara manufofin na gwamnatin Balewa da cewa, gwamnatin, ta yi watsi da akidun masu son sauyi ne, kuma ma, ta ki hada kai da gwamnatocin “yan sauyi a lokacin. Sai dai, masu wannan suka, a lokaci guda kuma sun furta cewa, shi Balewan, yana nuna matukar kaunarsa ga nahiyar Afurka, haka zalika, yana mai matukar mayar da hankali a kan duk wasu batutuwa da su ka shafi nahiyar ta Afurka (Fawale 2003, P. 40).

An gabatar da wasu daga masu suka tsagwaro, da kuma wadanda ke gwama suka da yabawa, haka kuma, akwai wadanda su ke, su kuma, masu yin yabo ne. Ka da mai karatu ya sha’afa, babban abinda wannan rubutu ke son haskawa, bai wuce irin damuwa gami da aiki tukuru a kasa, wanda jagororin Nijeriyar Jiya su ka nuna, ta fuskacin samar da, gami da inganta kyawawan manufofin Kasar, wajen mu’amalarta da Kasashen ketare, lamarin da dan Nijeriyar Yau, musamman wanda bai da masaniyar irin wadancan mu’amuloli sai ya dauka ma tamkar tatsuniyoyi ake gabatarwa.

Daga masu yabawa kyawawan manufofin gwamnatin ta Tafawa Balewa, akwai masu tunanin cewa, a matakin farko na manufofin Kasashen ketare da gwamnatin ke da, za a ga ko kadan babu wasu lamura na son zuciya da rashin kishin kasa da gwamnatin ta kunshe cikin manufofin (Hart 2009).

Yana da gayar kyawo mu shiga cikin wadancan manufofin da muke ta balokoko ko nanatawa an gabatar da su a Nijeriyar ta Jiya.

Exit mobile version