Daga Abubakar Abba,
Tsaikon da ake samu na bai wa manoman abinda ya kamata a ba su Kan lokacin da ya dace, ba karamar shafar fannin aikin noma yake ba a kasar nan.
Shugaba kungiyar manoma na Arewa Maso Yamma reshen jihar Kaduna, Alhaji Adamu Mohammed Makarfi, ne ya bayyana hakan a hirarsa da LEADERSHIP Ayau a Kaduna.
“Hakan ne kuma yake kawo wa a wasu lokutan idan an ba manoman bashi ba a kan lokaci ba, zaka ga cewar kudin sun yi asarar su, amfanin gonar yake lalace azo kuma ana cewa ana bin su bashi a kama su a daure su”.
“Misali, akwai na masu zaman kansu da suke barka da manoman da abinda ya kamata su bai wa manoma, suna ba su a kan lokacin da ya dace”.
“Ina kira ga gwamnati, musamman gwamnatin tarayya duk inda za ta yi wani tsaro na aikin noma, musamman na Anchor Borrowers, a nemi manoma na gaskiya, aje aga gonar su domin a tabbatar da cewa gonakin nasu ne”.
Ya kara da cewa, idan za a ba su daukin ka da ya kai watan biyar, watan hudu shi ne kolokulawa, duk abinda za a ba su, yadda za su zama cikin shirin yadda za zu yi noman yadda ya dace kuma a bunkasa shi.
Makarfi wanda kuma shi ne Sakatare Janar na kungiyar manoma masu yin noma don riba a a jihar ya ci gaba da cewa, “Yanzu muna cikin watan Fabirairu, duk inda aka ce an kai watan hudu ka ga an fara koma wa gona, domin daga watan uku, zamu fara shafar gonakan mu, mu zama cikin shiri idan ruwa ya sauka a watan hudu kuma nun tabbatar ya kai ayi shuka, za mu yi da izinin Allah, amma idan ba an yi wani tsarin da ya dace ba kuma a cikin hamzari, za a iya koma wa gidan jiya”.
Kan takin zamani na gwamnati kuwa, ya ce, “Duk da gwamnatin tarayya ta sa farashin buhun takin zamani daya kan naira 5,000, amma abin damuwa, an sayi takin buhu daya kan naira 15,000, zuwa yanzu, takin ya fara kai wa naira 15,000 wanda idan gwamnati ba ta shigo da hamzari ba ta yi wani abu hubbasa, abubuwa za su kara ta’zzara”.
A kan yawan Masarar da manomanta a kasar nan za su iya noma wa ta ta kuma wadaci kasar har da dabbobin da kuma Kaji ya ce, “A bisa kididdigar masana ta bangaren noman Masara, mu na neman tan miliyan sha shida zuwa tan miliyan ashirin”.
“Wannan, ya isa cimaka ga ‘yan Adam, dabbobi da Kaji na abinda su ke bukata na Masara, idan aka ce akalla an samu tan miliyan hamsin, ka ga ya yi ambaliya da akalla tan miliyan talatin”.
“A ganin mu duk wani zuwa da ake yi ta wani tattalin masana na samar da aikin yi, ba abinda zai samar da aikin yi kamar harkar aikin noma kuma idan ana bukatar Nijeriya ta bunkasa tattalin arzikin kasar ya karu, aikin yi ya karu, barazanar ta rashin aikin yi ya ragu, to a bunkasa harkar noma”.
Ya ce, abinda ya kamata a dauki noma sana’ar ba wai a noman ka wai don mutum ya ci a gidansa ba, ya kamata akalla, idan mutum ya samu kamar misali, buhu dari, zai iya amfani da akalla buhu goma, tamanin ya sayar, zai iya yin bukatunsa na iyalansa a cikin sauki”.
A kan noman rani ya ce gwamnati tun kafin hasashen da aka yi na cewa, ana sa ran za a samu ambaliyar ruwan sama a daminar bana take tunanin saboda gurbin da za a cike wajen noman na daminar da ta wuce, cewa, za a bunkasa harkar noman rani, inda ana cikin haka sai ga wannan hasashen yazo.
“Mu a ganin mu, da za a bunkasa harkar noman rani da mu na iya cewa, abinda za a iya samu ma a noman rani, zai fi abinda ake samu a daminar, amma, idan an yi kyakyawan tsari daga lokacin da daminar ta wace za a iya yin noman rani sau biyu a cikin wannan harkar”.
A kan gudanar da bincike a fannin noma ya ce,“Mu na ta kira ga gwamnati ta bai wa jami’oin kasar kudede masu yawa domin yin nazari na samo hanyoyin bunkasa noma”.
Ya ce, dukkan kasashen duniya da irin wannan nazari da su ke yi ne, nomansa ke bunkasa, musamman wajen samar wa da manoman su ingantaccen Irin noma.