Jinkirin Kai Daukin Jami’an Tsaro Ke Sa Mu Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Gwamnan Zamfara

Daga Hussaini Yero, Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Honarabul Bello Matawalle Maradun, ya bayyana cewa, Jinkirin kai daukin jami’an tsaro ne ya sa su dole suke sulhu da ‘yan bindiga.

Honarabul Matawalle ya bayyana haka a lokacin da tawagar Shugabannin kungiyar Gwamnonin Jamiyyar APC, suka kai masa ziyarar jaje na asarar rayuka a makon da ya gabata karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi Honarabul Abubakar Bagudu da Gwamnan Jigawa Honarabul Badaru.

A jawabin da ya gabatar, Gwamna Matawalle, ya bayyana jin dadinsa ga tawagar gwamnonin da suka kawo wa al’ummar Jihar Zamfara sakamakon harin ‘yan bindiga.

A cewar Gwamna Matawalle daukar matakin sulhun da ‘yan bindiga ya zama dole sakamakon jinkirin kai daukin jami’an tsaro a lokacin da ‘yan bindiga ke kai hare-hare kuma wannan shi ne matsayarmu. “ Sannan kuma na gaya wa Shugaban kasa Muhammad Buhari a ganarwar da muka yi da shi.

“Shugaban kasa ya kuma tabbatar mani da cewa, a kan matsalar tsaro a Zamfara ko da yaushe kofarsa a bude take don samun tattaunawa da shi wajen magance matsalar.

Don haka yanzu za mu yi kwana uku don tattaunawa da jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a kan harkar tsaro da ‘yan sa kai don ganin an kawo karshe mawuyacin halin da muke ciki da yardar Allah.

Matawalle, ya kuma mika sakonsa ga shugabanin gwamnonin, zuwa ga Shugaban kasa Muhammad Buhari, da ya ba kowane gwamna damar samar da hanyoyin magance matsalar tsaro jiharsa.

A nasa jawabin shugaban kungiyar gwamnonin, Sanata Bagudu, ya bayyana cewa, suna cikin taro a Abuja tare da Gwamna Matawalle aka bugo masa waya cewa, ‘yan bindiga sun kai hare-hare wanda ya yi sanadiyyar rayuka da dama wannan ne ya sanya ya nemi afuwa daga ficewa daga taron ya dawo Zamfara, ddon haka muka ga ya dace mu biyo shi don jajanta wa al’ummar jihar Zamfara, a kan asarar rayukan da aka yi, da fatan Allah ya ji kan wadanda suka rasu, ya kuma kawo mana karshen wadannan ‘yan bindiga amin.

Exit mobile version