Jirgin kasa mai saurin tafiya dake aiki da dare, wanda ya hada birnin Beijing da Shanghai da yankin musamman na Hong Kong da ke kudancin kasar Sin, ya fara aiki a jiya Asabar, inda ya rage yawan lokacin tafiya.
Sabon jirgin ya rage lokacin da ake dauka na tafiya tsakanin Beijing da Hong Kong, daga sa’o’i 24 da minti 31, zuwa sa’o’i 12 da minti 34, inda na shanghai zuwa Hong Kong ya ragu daga sa’o’i 19 da minti 34 zuwa sa’o’i 11 da minti 14.
A baya, jirage masu tafiya mai nisa daga tashar West Kowloon ta Hong Kong zuwa tashar jirgin kasa ta yammacin Beijing na aiki ne da rana kadai. Amma da wadannan sabbin jiragen kasa masu tafiyar dare, fasinjoji na iya cin gajiyar tsarin nan na yin barci tsawon tafiya, domin samun karin saukin tafiyar. Haka kuma za su iya tashi daga kowanne daga cikin biranen a duk ranakun Juma’a zuwa Litinin da dare tare da isa inda za su je washegari da safe. (Fa’iza Mustapha)