A kwanan nan ne jirgin kashe gobara mai lakabin “modern Ark 60” (MA60) na kasar Sin ya kammala gwajinsa na farko, in ji kamfanin da ya kera jirgin, kamfanin sarrafa jiragen sama na kasar Sin (AVIC).
Jirgin na ayyukan da suka hada da kashe gobara da ruwa, sadarwa daga sama da rigakafin gobara da sa ido a matsayinsa na babban jirgin kashe gobara mai matsakaicin fuka-fuki. Yana kuma iya jigilar maaikata da kayayyaki a lokutan ayyukan ceton gaggawa, in ji AVIC.
Jirgin yana tafiya da nisa kuma cikin sauri, da tashi sama a karamin tazara, abin dagoro a yayin da yake tashi sama sosai, da kuma jigila tsakanin yankuna masu nisa da juna. (Mai Fassarawa: Yahaya Babs)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp