Jirgin ruwan kasar Sin mai aikin jiyya ko “Peace Ark”, wanda aka yiwa aikinsa lakabi da “Mission Harmony-2024” a Turance, ya bar gabar tekun birnin Cotonou na kasar Benin a jiya Alhamis, bayan ya kammala aikinsa a kasar.
A wa’adin aikin sa na kwanaki 7, likitocinsa sun yiwa marasa lafiya tiyata 137, tare da jiyyar mutane 8,122, da binciken lafiya ga mutane 3,297, adadin da ya kai sabon matsayi, tun lokacin da jirgin ya fara aikinsa.
- NSCDC Ta Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga A Kano
- Hatsarin Jirgi Ya Sa Mataimakin Shugaban Kasa Ya Soke Ziyarar Amurka
Ziyarar jirgin a kasar Benin ta jawo hankalin gwamnatin kasar matuka, saboda ganin cewa, wannan shi ne karo na farko da jirgin ya kai ziyara kasar. Jami’an soja da dama sun shiga jirgi, don halartar ayyuka masu nasaba.
Mataimakiyar shugaban kasar Benin Mariam Chabi Talata, ta jinjinawa taimakon da jami’an kiwon lafiya na kasar Sin suke bayarwa, wajen tabbatar da kula da lafiyar jama’ar kasar.
Yanzu haka dai jirgin na “Peace Ark” yana kan hanyarsa zuwa kasar Mauritaniya, wato zango na 11 da zai isa domin ci gaba da gudanar da aikin ba da jinya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp