Kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS ya yi kira da a karfafa gwiwa kuma a jajirce wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa da ake fafatawa, yayin da halin da ake ciki a yanzu ya kasance mai tsanani da sarkakiya.
An yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwar da aka cimma a cikakken zaman taro na hudu na kwamitin koli dake kula da ladabtarwa na JKS karo na 20, wanda aka gudanar daga ranar Litinin zuwa ta Laraba a Beijing.
Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, Xi Jinping, ya halarci zaman, inda ya gabatar da muhimmin jawabi. (Mohammed Yahaya)