JNI Ta Gabatar Da Sabon Limamin Masallacin Kungiyar Ga Sarkin Lokoja

Sarkin Lokoja

Daga Ahmed Muhammed Danasabe,

Jami’an kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen jihar Kogi, karkashin shugabancin Ambasada Usman Bello a ranan larabar data gabata, sun kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji( Dr) Muhammadu Kabir Maikarfi 111, a fadarsa, inda suka gabatar masa da sabon limamin masallacin kungiyar da aka bude kwanakin baya a sakayariyar kungiyar dake Lokoja.

A ranan 24 ga watan Yuni ne, kungiyar ta JNI ta nada Alhaji Usman Tauheed a matsayin sabon limamin masallacin kungiyar.

Da yake jawabi, shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam( JNI) reshen Jihar Kogi, Ambasada Usman Bello, ya shaidawa Sarkin Lokoja, cewa sun kawo ziyara fadansa ne domin gabatar da sabon limamin masallacin da kungiyar ta nada, wato Alhaji Usman Tauheed da kuma nuna godiyarsu ga Sarkin a bisa turo babban limamin garin Lokoja, Sheikh Aminu Shaban wanda ya rantsar da sabon limamin masallacin kungiyar ta JNI.

Ambasada Usman Bello ya kuma yabawa Sarkin na Lokoja, a bisa kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar masarautarsa duk da banbancin addini dake tsakanininsu,yana mai sanar da Sarkin cewa a nata bangaren, kungiyar ta JNI na bakin kokarnta wajen hada kawunan al’ummar musulmin jihar Kogi da kuma tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a tsakaninin addinai mabanbanta dake jihar tare da hadin gwiwar kungiyar kiristoci ta CAN.

Da yake mayar da jawabi, mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi 111, ya godewa shugabannin kungiyar ta JNI a bisa ziyarar da kuma gabatar masa da sabon limamin masallacin kungiyar, Alhaji Usman Tauheed.

Ya kuma bukace su dasu ci gaba da kyakkyawan ayyukan alherin da suke yi na hada kan al’ummar musulmi da kuma tabbatar da zaman lafiya a tsakaninin addinai mabanbanta.

A karshe Sarkin na Lokoja ya sanyawa sabon limamin masallacin kungiyar albarka.

Har ila yau, kungiyar ta JNI ta ziyarci Khalifa, mai shari’a Nuruddeen Yusuf Abdallah, wanda ya dawo gida daga neman magani a kasar Misra( Egypt).

Cikin tawagar kungiyar ta JNI a yayin ziyarar, akwai shugabanta, Ambasada Usman Bello da sakatare, Alhaji Isah Adeboye da babban limamin masallacin kungiyar, Alhaji Usman Tauheed da jami’ain yada labarai na kungiyar, Alhaji Suleiman Ibrahim da kodinetan kungiyar mai kula da Lokoja da Kotonkarfe da dai sauransu.

Exit mobile version