Mai koyar da tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya, Jose Peseiro ya shafe watanni shida yana aiki ba tare da an biya shi albashi ba kamar yadda rahotanni suka bayyana wanda hakan wani koma-baya ne.
Kocin mai shekara 62 wanda ya soma aiki tun a watan Mayu bai fito fili ya gabatar da korafinsa ba game da hukumar kwallon kafa ta Nijeriya kan kin biyansa albashinsa, sai dai a martanin da hukumar kwallon kafa ta kasa ta mayar, ta bayyana cewa ta soma samar da tsare-tsare kan yadda za ta biya basussukan da ake binta.
- Kasar Sin Za Ta Kafa Karin Yankunan Misali 29 Na Inganta Shigo Da Kayayyaki Kasar
- Manoman Alkama 200 Za Su Amfana Da Shirin NALDA A Jihar Jigawa
Kamar yadda yake, dama dai akwai wadanda ke bin wannan hukumar kudi kamar tsohon mai koyar da tawagar wato Gernot Rohr wanda shi ne ya gabaci Peseiro da kuma wasu ‘yan wasan na Nijeriya
Wakilin mai koyarwa Peseiro ya bayyana cewa alawus-alawus dinsa kadai ya karba wanda a hakan abin damuwa ne saboda haka akwai bukatar kamar yadda wani ma’aikacin hukumar kwallon kafar ya shaida.
A ka’ida dai ma’aikatar wasanni ce ke biyan albashin mai koyarwa, amma sun yi sauri sun fito da wani sabon tsari da hadin kan ma’aikatar domin warware batun albashin a wannan makon da ake ciki.
Ma’ikatar wasanni ta kasa wadda ita ke da alhakkin biyan Peseiro ta dora laifin kan tsaiko da aka samu daga gwamnatin tarayya wurin samun kudin, kuma wani mai bayar da shawara ga ministan wasanni na kasar Sunday Dare ya tabbatar da cewa za a biya kocin ba da dadewa ba
Sai dai daman ba wannan ne karon farko ba da ake korafin kin biyan kocin kwallon kafa albashinsu a kan kari ba, domin akwai masu horar da kungiyar kwallon kafan Nijeriya da dama da har suka bar aiki suna bin bashi ba tare da an biya su ba.
Daga cikinsu akwai Christian Chukwu da Augustine Eguaboen da Samson Siasia da Sunday Oliseh da Florence Omagbemi da marigayi Shaibu Amodu kuma marigayi Stephen Keshi, kuma har yanzu dai Rohr yana bin NFF kudi. Haka kuma akwai ‘yan wasan Nijeriya maza da mata da ke bin hukumar kudi.
Dan wasan Super Eagles ba su ji dadi dangane da kin biyansu garabasa da kuma alawus dinsu na tun shekarar 2021 ba. Haka kuma ita ma kungyiar Super Falcons na jiran NFF da ma’aikatar wasanni su biya su bashin da suke bi na gasar kwallon kafa ta mata ta Afrika wato Wafcon.
Ko a watan Yuli sai da ‘yan wasan Nijeriya mata suka kaurace wa atisaye kafin su buga wasan da suka zama na uku a gasar WAFCON saboda kin biyansu alawus dinsu da ya kamata a biya su tun lokacin da aka kammala gasar.