Juventus ta katse yarjejeniyar kwantiragi tsakaninta da Paul Pogba a hukumance, ƙungiyar ta Serie A ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a jiya Juma’a.
Pogba na shirin komawa fagen ƙwallon ƙafa bayan dakatarwar da aka yi masa na tsawon shekaru hudu saboda gwajin maganin da aka yi mashi bayan rage tsawon lokacin zuwa watanni 18.
An Kwashe Wa Juventus Maki 10 A Gasar Seria A
De Ligt Ya Koma Bayern Munchen Daga Juventus
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ƙungiyar Ƙwallon ƙafa ta Juventus da Paul Pogba sun sanar da cewa sun amince da dakatar da kwantiragi tsakanisu, wanda zai fara daga 30 ga watan Nuwamba na shekarar 2024.
Yanzu haka tsohon ɗan wasan na Manchester United ya fara atisaye a ƙashin kansa a fatan da yake yi na dawowa fagen ƙwallon ƙafa nan ba da jimawa ba.