Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta ayyana dokar ta-ɓaci a faɗin yankin.
Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray ne, ya bayyana haka a ranar Talata, yayin taron kwamitin sulhu da tsaro na ƙungiyar karo na 55 da aka yi a Abuja.
- 2027: Ganduje Ya Gargaɗi Mambobin APC Kan Fara Tallata Masu Neman Takarar Gwamna Da Wuri
- Tinubu Ya Bai Wa Jami’an Tsaro Umarnin Ceto Sauran Ɗaliban Neja Da Ke Hannun ‘Yan Bindiga
An kira taron ne saboda yawan juyin mulki da ake ta fuskanta a wasu ƙasashen yammacin Afirka.
ADVERTISEMENT
Touray, ya ce waɗannan abubuwa sun nuna buƙatar ƙasashen ECOWAS su sake nazari sosai kan makomar dimokuraɗiyya a yankin, da kuma muhimmancin ƙara zuba jari a harkar tsaro.
Karin bayani na tafe…














