Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci tawagar malaman da suka fara tattauna yadda za a samu sulhu da daidaito kan rikicin shugabanci da ke faruwa a jamhuriyyar Nijar da su sake komawa kasar domin kulla kyakkyawar yarjejeniya.
Bayan wata ganawar sirri da shugaban ya yi da Usta Abdullahi Bala-Lau, jagoran tawagar malaman, Tinubu ya ce manufar matakin shi ne don guje wa zuwa ga amfani da karfin soja wajen dawo da mulkin demukuradiyya a Nijar.
- Hatsarin Kwale-kwale Ya Hallaka Rayukan Mutum 12 A Nasarawa, Majalisa Ta Jajanta
- Tarihi Zai Dorawa Japan Alhakin Sakin Gurbataccen Ruwan Nukiliya Zuwa Teku
A nasa bangaren, Bala Lau ya ce, Tinubu ya amshi dukkanin shawarorin da suka bayar na kauce wa sanya karfi da matakin soja musamman da yake kasashen makwantan su na da alaka da ta jimana tsakani.
“Shugaban ya karbi dukkanin shawarorinmu na kauce wa kowace irin matakin sanya karfi. Kamar kuma yadda muka tattauna da shugabannin Nijar da suka amince cewa za su kauce wa rikici, shi ma shugaban kasan ya amince da hakan.
“Wannan dalilin ne ma ya sanya shi ya sake turamu da mu koma Nijar domin cigaba da tattaunawa kan yadda za a dawo da mulkin demukuradiyya a kasar. Ya kuma umarci mu da mu tunatar da shugabannin sojojin dangane da matakan ECOWAS da su ke kasa,” Bala-Lau ya fada.
Ya ce, shiga tsakanin da malaman suka yi ta haifar da sakamako mai kyau, ya kara da cewa har ta hakan sojojin Junta suka aminta har suka ganawa da wakilan ECOWAS karkashin Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) da Sultan Abubakar Sa’ad III.
Bala-Lau ya ce don haka Ulama za su koma Nijar su ci gaba da nemo hanyoyin kawo karshen matsalar, ya kuma kara da cewa sun fashimci ana zuwa matakin yaki ne idan aka kasa cimma matsaya a dukkanin zaman sasantawa.