Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya roƙi ’yan siyasar Kano da su guji rikici da rabuwar kai saboda siyasa, inda ya bayyana cewar zaman lafiya ya fi komai muhimmanci a rayuwa.
Shettima, ya yi wannan kira ne lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, mahaifin shugaban jam’iyyar APC a jihar, Abdullahi Abbas.
- Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia
- Maganin Karin Kiba
Ya bayyana cewa rikicin Boko Haram ya jefa jiharsa ta Borno cikin wahala, kuma ba ya so a ga irin hakan ta faru a Kano.
Ya ce, “Idan rikici ya taso a Kano, to Arewa baki ɗaya za ta shiga matsala, domin Kano ita ce uwar Arewa baki ɗaya.”
A lokacin ziyarar, Shettima ya samu rakiyar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da shugabannin jam’iyyu daban-daban.
An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp