Khalid Idris Doya" />

KADCCIMA Ta Nemi Gwamnati Ta Farfado Da Noman Auduga A Nijeriya

Cibiyar kasuwanci, masana’antu, tama da karafa gami da ayyukan noma ta Jihar Kaduna (KADCCIMA), ta ce, kara yawan noman auduga shi ne mataki na farko na farfado da masana’antun kasar nan.
Daraktan cibiyar, Alhaji Usman Saulawa, ne ya fadi hakan a sa’ilin da shugabannin cibiyar suka kai ziyarar ban girma ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), a Abuja.
Ziyarar wata sashe ne na yayatawa al’umma bukin kasuwar Duniya ta 40 wacce take ci a Kaduna, a duk shekara, wacce kuma za ta fara ci daga ranar 28 ga watan Maris zuwa 7 ga watan Afrilu.
Babban manajan darakta na kamfanin na NAN, Mista Bayo Onanuga, babban editan kamfanin, Mista Idris Abdurrahman da sauran wakilan kamfanin ne suka karbi bakuncin tawagar.
Saulawa ya ce, a shekarun 1960, Nijeriya tana kan hanyar zama jagoran kasashen Afrika, ta fuskacin masana’antun saka tufafi, inda take da kimanin manoman auduga milyan biyu a cikin kasar nan.
Sai dai ya ce, tsare-tsaren da ba su dace ba, da yanda farashin ya yi ta kwan-gaba, kwan-baya, a karshen shekarun 1990, ya shafi harkokin masana’antun, ta yanda har kamfanonin masana’antun suka fara rufewa.
Ya kuma yi tilawar yanda dubannan ma’aikatan da suke aiki a masana’antun suka rasa ayyukan su, manoman auduga kuma aka barsu da ita jibge babu masu saye, hakan ya sanya suka bar noman audugan suka kama wasu abubuwan na daban.
Saulawa ya yabawa sabon tsarin babban bankin kasar nan (CBN), inda ya hana shigowa da kayayyakin tufafi a cikin kasar nan.
Ya ce, hakan zai iya sanyawa a farfado da noman audugan da saka tufafin, kamar dai yanda hakan ya faru ta fuskacin noman shinkafa a kasar nan.
Ya yi tilawar yanda lamarin ya kasance a lokacin da babban bankin ya yi hani kan shigowa da shankafa kasar nan, yanda mutane suka fusata da hakan, saboda kowa ya saba da cin shinkafa ‘yar waje ne, “amma a halin yanzun, sama da kashi 60 na shinkafar da ‘yan Nijeriya ke ci, duk a cikin kasar nan ne ake noma ta.”
Saulawa ya yi hasashen irin hakan ne zai faru da noman auduga, masana’antun saka da tufafi da suka shafi tattalin arzikin kasa duk za a inganta su da sama masu isassun kudade da ingantaccen irin shuka.
“Mu a wajen mu, KADCCIMA, hakan kuduri ne mai kyau. Na san masu shigowa da wadannan kayayyakin ba za su yi murna da hakan ba, amma mun yi imani da cewa, tilas ne a sami sadaukarwa a wasu fannonin.
“Hakan, saboda shigowa da kayayyakin masana’antun sakan marasa inganci suna cikin abubuwan da suka lalata mana tattalin arzikinmu.
“Masu shigowa da kayayyakin masana’antun na saka sun taimaka wajen lalata mana kamfanonin masana’antun namu, wadanda suke rayuwa da kyar.
“Hana shigowa da kayayyakin masana’antun sakan zai tilasatawa masu shigowa da kayan masana’antun da su kafa na su kamfanonin sakan a nan Nijeriya, domin su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikinmu,” in ji shi.
Saulawa ya ce, hakan kuma zai taimaka kasarmu ta yi tsimin kudadaenta na canji a waje wanda za a iya amfani da su a kan wasu mahimman abubuwan musamman a sashen kere-kere.
Kididdigan bankin na CBN, ya nuna cewa, sama da dalar Amurka bilyan hudu ne ake kashewa a duk shekara wajen shigowa da kayayyakin masana’antun na saka da kuma wasu dinkakkun kayayyakin, alhalin da yawa daga cikin masana’antun saka na kasar nan da masu yin tufafin sawa duk suna ta mutuwa.
Hakan ne ya sanya babban bankin ya yanke shawarar hadawa da masu shigowa da duk wani nau’i na kayayyakin masana’antun sakan a cikin jerin kayayyakin da aka hana masu samun kudaden canji na waje a kan farashin Naira 306.95 kan kowace dalar ta Amurka guda.
A shekarar 2015, babban bankin ya sanya iyaka ga samun kudaden canjin a kan kayayyaki 41 wadanda ana iya samar da su a cikin kasar nan, tun daga wancan lokacin ne ake ta yin kari a kan yawan wadannan kayayyakin.
Tun daga wancan lokacin babban bankin ya kara yawan kayan da ba a ba su cin moriyan kudaden canjin zuwa 43, inda aka shigar da takin zamani da kayan masana’antun na saka a cikin su.

Exit mobile version