A Nijeriya akwai filayen sauka da tashin jirage masu yawa amma kuma sai dai kuma ashe ta gina ne ba ta shiga ba kamar yadda Olubunmi Kuku, Manajan Darakta na Hukumar Kula da Filayen Jirgin Sama ta Najeriya (FAAN), ya bayyana, kawai filayen jirgin sama uku daga cikin 22 na Nijeriya na ƙasa da ƙasa ke samun riba.
Yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels TV a shirin “The Morning Brief” yau Talata, Kuku ya jaddada matsalolin kuɗi da yawancin filayen jirgin sama na ƙasar ke fuskanta. Ya bayyana cewa duk da matsalolin samun riba, wasu jihohin arewa da kudu maso yamma na gina sabbin filayen jirgin sama.
- Yadda Aka Yi Bikin Kaddamar Da Littafin Babban Editan LEADERSHIP A Abuja
- 2024 Hajj: Za A Ƙaddamar Da Tashin Maniyyata Zuwa Saudiyya Karon Farko A Kebbi
Kuku ya bayyana cewa FAAN na tallafa wa sauran filayen jirgin sama 19 don tabbatar da ci gaba da aikinsu. Ya jaddada cewa wannan tsarin na iya faɗaɗa zuwa sabbin filayen jirgin sama da ake gina wa. “Muna tallafa wa sauran filayen jirgin sama 19 a yau kuma a mafi yawan lokuta, za mu tallafa wa wasu daga cikin sabbin filayen jirgin sama da ake ginawa,” inji Kuku.
Baya ga kula da filayen jirgin sama 22, FAAN na tallafa wa kimanin filayen jirgin sama shida ko bakwai da gwamnoni ko masu zaman kansu ke kula da su da tsaron jiragen sama da kuma ayyukan ceto. Kuku ya nuna cewa filayen jirgin sama uku ne kawai ke samun riba kuma suna bayar da gudunmawa sosai wajen tallafa wa kamfanonin filayen jirgin sama da FAAN ke gudanarwa.