Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin wannan gwamnati wajen bai wa kafafen yaɗa labarai ‘yancin su, ba tare da takunkumi ko dabaibayi ba.
Ya ce kafafen yaɗa labarai sun taka muhimmiyar wajen tabbatar da kafuwar turakun dimokiraɗiyyar ƙasar nan, don haka abu ne da ya zama dole a a yi riƙo da kafafen yaɗa labarai saboda tasirin su.
Ministan ya bayyana haka ne a ranar Talata, lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Cibiyar Kare Haƙƙin Jaridu da ‘Yan Jarida ta Duniya (IPI), a ƙarƙashin shugaban ta, kuma Babban Editan jaridar Premium Times, Alhaji Musikilu Mojeed.
IPI ta kai ziyara ne a ranar Talata, 19 ta Disamba, a ofishin ministan da ke Abuja.
IPI ƙungiya ce ta manyan editocin jaridu na duniya, masu kafafen yaɗa labarai da kuma fitattun ‘yan jarida.
Babban dalilin kafa ƙungiyar shi ne kare haƙƙin aikin jarida tare da tsayawa kan kare aikin jarida da ‘yan jarida daga dukkan wata barazanar da ka iya tunkarar su.
Ministan ya ƙara nanata matsayar Shugaba Tinubu dangane da ‘yancin kafafen yaɗa labarai, tare da cewa shi kan sa shugaban tsohon ɗan gwagwarmayar kare ‘yancin dimokiraɗiyya ne, don haka ya na da dukkan ruwa da tsaki wajen nuna goyon bayan ‘yancin kafafen yaɗa labarai da ‘yan jarida.
Kuma ya yi alƙawari cewa gwamnatin sa ba za ta taɓa yi wa aikin jarida ƙarfa-ƙarfa ba.
Idris ya ce dimokiraɗiyya a Nijeriya na buƙatar nagartacciyar alƙibla, wadda kuma gwamnati ke neman gudunmawar dukkan masu karsashin ƙara mata nagarta, ciki kuwa har da jaridu, kafafen yaɗa labarai da ‘yan jarida su kan su.
Ya ce yi wa wannan tsari garambawul nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa, a dunƙule.
Daga nan ya yi yabo da jinjina ga shugaban IPI dangane da zaɓen sa da aka yi ya jagoranci cibiyar.
Ya yi kira ga Mojeed da ya yi amfani da ƙwarewar sa ta aikin jarida wajen yi wa IPI kyakkyawan jagoranci.
Tun da farko, sai da Shugaban na IPI, Musikilu Mojeed, ya shaida wa ministan cewa a yanzu ana samun cigaba a farfajiyar kafafen yaɗa labarai, don haka ana yi wa aikin jarida kyakkyawar fata nagari.
Daga nan ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da kare rayuka da lafiyar ‘yan jarida a duk inda suke aiki.
Ya kuma tabbatar wa da Idris cewa IPI za ta ba shi goyon baya, musamman kasancewa ya na ɗaya daga cikin membobin farko da su ka kafa cibiyar.