Kafar sada zumunta ta WhatsApp mallakin kamfanin Meta ta samu matsala ta daina aiki, tun misalin karfe 6:45 na safe agogon Nijeriya.
Mutane da dama sun shiga rudani kan ganin cewar kafar ta tsaya cak ba ta aiki.
- Buhari Ya Bai Wa Ministan Ruwa Wa’adin Wata 3 Don Kawo Karshen Ambaliyar Ruwa A Nijeriya
- Sin Ba Za Ta Shigo Da Salon Neman Ci Gaba Na Sauran Kasashe Ba
Fiye da mutum 12,000 ne suka wallafa ƙorafi kan hakan cikin ƙasa da awa ɗaya, a cewar sashen fitar da bayanai na manhajar.
Wasu da farko sun dauka cewar kamfanin sadarwarsu ne ya samu matsala wanda kowa ya dinga shiga neman layin da zai yi amfani da amma duk da haka ba ta sauya zani ba.
Wannan tsayawa da kafar sadarwar ta yi ta kawo cikas ga masu harkar kasuwanci da kuma sauran daidaikun mutane da ke amfani da kafar.
Akalla mutane biliyan biyu ne ke amfani da kafar sada zumunta ta WhatsApp a fadin duniya.
A shekarar da ta wuce irin wannan matsala ta taba afkuwa idan kafafen sada zumuntar WhatsApp da Facebook suka samu matsala suka daina aiki.
Lamarin da ya sanya kamfanin na Meta ta tafka babbar asara.