Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Kafofin Watsa Labaran Ketare: Matakan Birnin Beijing Na Dakile Yaduwar COVID-19 Za Su Zama Abin Koyi

Published

on

Tun lokacin da aka gano sabbin masu dauke da cutar COVID-19 a birnin Beijing a ranar 12 ga watan nan, jaridar The New York Times ta kasar Amurka da gidan rediyon ABC na Australiya da jaridar South China Morning Post ta Singapore sun yaba wa matakan da gwamnatin birnin Beijing ta dauka wajen dakile cutar.

A ranar 19 ga wata, jaridar The New York Times ta yada labarai game da yadda birnin ke tinkarar wannan annoba. Inda jaridar ta ce an dauki matakai yadda ya kamata, tun lokacin da aka gano mai dauke da cutar a Beijing, domin magance bazuwar ta cikin gaggawa.

A wannan karo, ba a killace birnin Beijing baki daya ba, sai dai an dauki matakan kandagarki a matsayin koli, a wuraren da suka fi fama da matsalar yaduwar cutar.

Hakan ya sa, wasu kantuna, da dakunan cin abinci, da dakunan gyaran gashi suke ci gaba da ayyukansu kamar yadda suka saba, kuma al’ummomin birnin su ma ba su dakatar da ayyukansu ba.

Jaridar New York Times ta kuma bayyana cewa, birnin Beijing ya dauki wadannan matakai ne bisa fasahohin da kasar Sin ta samu, na yaki da cutar a watanni da dama da suka gabata.

Ta kuma ce idan aka cimma nasarar dakile yaduwar cutar a birnin na Beijing, wadannan matakai za su kasance abun koyi ga kasashe daban daban, inda tuni wasu kwararrun kasa da kasa da dama suka nuna amincewa da hakan.

Bisa labarin da jaridar South China Morning Post (SCMP) ta fidda, a lokacin da wasu kasashen Asiya suke son farfado da tattalin arzikinsu, za su gamu da matsalar sake dawowar cutar COVID-19. Shi ya sa, matakan da aka dauka a birnin Beijing za su zama abin koyi gare su.

Sannan, a Talata, gidan rediyon ABC na kasar Australia ya yabawa birnin Beijing dangane da matakai masu inganci da ya dauke wajen dalike yaduwar cutar, inda ya fidda sharhi mai taken “Matsala iri daya da ake fuskanta, amma matakai iri daban da aka dauka”.

Cikin sharhin, gidan rediyon ABC ya bayyana cewa, yayin da ake fuskantar matsalar sake yaduwar cutar COVID-19, birnin Beijing bai bata lokacinsa ba wajen tsayar da yaduwar cutar. Cikin wannan birni mai kunshe da mutane sama da miliyan 20, ana gudanar da aikin dakile yaduwar annoba cikin unguwanni yadda ya kamata, yayin da kuma ake yin gwajin cutar cikin sauri.

A sa’i daya kuma, ana ci gaba da samun karin masu dauke da cutar, da adadinsu ya kai sama da goma a kowace rana cikin kwanaki 7 da suka gabata a birnin Melbourne. Shi ya sa, gidan rediyon ABC na kasar Australia na fatan birnin Melbourne zai iya koyon fasahohin birnin Beijing, domin magance dawowar cutar COVID-19.

(Mai Fassarawa: Maryam Yang)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: