Connect with us

KIWON LAFIYA

Kai Cibiyoyin Kiwon Lafiya Zuwa Matakin Kasa Da Kasa Ka Iya Rage Mace-Macen Jarirai Da Mata Masu Juna Biyu, Inji Masana

Published

on

An bayyana cewar yin duk mai iyuwa don tabbatar da kai cibiyoyin kiwon lafiya zuwa matakin kasa da kasa a matsayin hanya daya ta kawo karshen yawaitar mace-macen jarirai da mata masu nakuda a cikin al’umma.
Babban Jami’in ilmantarwa kan kiwon lafiya a karamar hukumar Jama’are da ke jihar Bauchi, Alhaji Sabo Buba shine ya shaida hakan a wajen taron horaswa da ke ci gaba da gudanuwa na tsawon kwanaki biyar da aka shirya domin ilmantar da mazaje kan hanyoyin rage yawaitar mace-macen jarirai da mata a lokacin da suke yukurin haihuwa, taron wanda ke gudana a can karamar hukumar ta Jama’are.
Alhaji Sabo Buba ya bayyana cewar a jihar Bauchi akwai cikakken daman a rage yawaitar mace-macen mata da jariransu matukar aka daukaka darajar cibiyoyin kiwon lafiya da suke cikin al’umma zuwa matakan da ya dace a kaisu domin samar da yanayin aiki nagartaccen.
Ya ce, ta hakan ne kawai za a iya shawo kan matsalolin da suke akwai dangane da yawaitar mutuwar gabani ko bayan haihuwar jarirai.
Ya bayyana cewar babban makasudin samar da cibiyoyin kiwon lafiya daman sune domin rage yawaitar mutuwa, samar da waraka da kuma kula da majinyata hade da basu shawarorin da suka dace da rayuwarsu, musamman ga mata masu juna biyu.
Daga bisani ya kirayi dukkanin wadanda suke da alhakin kula da cibiyoyin jinya da su ke yin aiki domin al’umma, yana mai shaida cewar ladarsu na ga Allah, inda ya bayyana cewar zage damtse don bayar da gudunmawa kan harkar lafiya zai bayar da dama a samu cimma nasarorin gudanar da kiwon lafiyan jama’a cikin sauki.
Ya yi amfani da damar wajen jinjina wa gwamnatin kasar Kanada ta cikin shirinta na ‘Plan International’ a bisa gudunmawar da suke bayarwa na tabbatar da habaka kiwon lafiya da ilmantar da jama’a dangane da muhimmancin lafiyarsu a jihar ta Bauchi.
Alhaji Sabo Buba ya tabbatar da cewar karamar hukumar Jama’a za ta sake aza damban ci gaba da kyautata sha’anin kiwon lafiya domin ci gaba da kare rayuka da lafiyar jama’an da suke rayuwa a yankunan.
Advertisement

labarai