Kakakin gwamnatin babban yankin kasar Sin, ta yi tsokaci game da zaben yankin Taiwan da ya gudana a jiya Asabar, wadda ta yi nuni ga aniyar al’ummar yankin na tabbatar da zaman lafiya, daidaito da samun ingantacciyar rayuwa.
Zhu Fenglian, wadda ita ce kakakin ofishin lura da harkokin yankin Taiwan na majalissar gudanarwar kasar Sin, ta kara da cewa, babban yankin kasar Sin zai ci gaba da aiki tukuru tare da al’ummun Taiwan, wajen ganin an cimma nasarar wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba tsakanin dukkanin yankunan dake gabobi biyu na zirin Taiwan, da ba da gudummawar ciyar da rayuwar al’ummar dukkanin sassan zirin Taiwan gaba.
Zhu Fenglian ta kara da cewa, babban yankin kasar Sin na matukar adawa da batun samun ‘yancin yankin Taiwan, da tsoma bakin sassan kasashen waje cikin harkokin yankin. Za a kuma yi duk mai yiwuwa, wajen ganin bakin dayan kasar Sin ta samu farfadowa yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)