A makon da ya gabata Amurka ta fitar da gargadi ga ‘yan kasarta da ke zaune a Nijeriya inda ta yi kira a gare su da su yi taka-tsantsan kan yiwuwar “fuskantar barazana” a wasu manyan otal-otal din kasar nan.
Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin jin dadinta kan gargadin da Amurka ta yi wa ‘yan kasarta mazauna Nijeriya kan su yi taka-tsantsan yayin da suke zaune a kasar.
Hukumomi sun ce gargadi irin wannan zai haifar da rudani ya kuma shafi tattalin arzikin kasar.
Ko da yake, shawarar da Amurka ta bayar har ila hau ta ce jami’an tsaron kasar na daukan matakan dakile duk wani hari.
Yayin da yake wani jawabi a Abuja, Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya ce wannan gargadi da Amurka ta fitar zai iyara mayar da hannu agogo baya a yunkurin da gwamnati ke yi na janyo hankulan masu saka hannun jari.
Ya kara da cewa, gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta kare lafiyar dukkan masu ziyara a kasar.