Duk da rashin wadataccen lokaci da na ke ciki, sakamakon tafiyata Umrah wanda na ke kan gudanar da aiyukan ibada, sai kawai na yi kicibus da wata tattaunawa da gidan rediyon BBC Hausa ta yi da korarren sakataren hukumar da ke kula da tallafa wa manyan makarantu a Nijeriya (TETFUND), Dakta Baffa Bichi, bayan korarsa da gwamnatin mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi. Duk da cewa ba komai a cikin tattaunawar face irin faganniya, rudewa irin ta marasa gaskiya, da kame-kame irin wanda ta kare masa.
Amma duk da haka sabo da kokarin taba mutuncin wadanda duniya ta yiwa shaida na kwarai, na yanke shawarar na yi masa martani, tun da ya san, na san lokacin da ya ke neman gindin zama a wajen shi mai girma babban Ministan ilimi Malam Adamu Adamun da yanzu ya ke neman ciwa mutunci don an tsigeshi a bisa dalilan da ake ganin su ne mafita ga kawo ci gaban kasa. Tattare da shi kansa ya san laifukansa ba boyayyu ba ne a cikin cikin wannan kasa, amma ai zai yi wa EFCC bayaninsu.
Korarre sakataren TETFUND ya manta ‘yan uwansa malaman jami’a sun sha kokawa da shi ta hayar rubuce-rubuce tun bayan zamansa a kan wannan kujera. Mai makon ya maida hankalinta don magance dinbin matsalolin manyan makarantun sai ya mayar da hankali wajen sarrafa kudade masu yawa da kowa ya san baya da su kafin zamansa shugaban wannan babbar ma’aikata, wanda kuma duk duniya ta shaida wannan gwamnatin da sanya ido kan masu babakere, Bichi ya kafa wata kungiya mai reshe a jihohi 36 mai suna ‘One 2tell Ten’ yana kashe miliyoyin nairori wajen tafiyar da kungiyar, da sauran tulin bayanan da suke kansa na abubuwa da yawa.
A zatonsa hakan zai iya ba shi damar zaman tabbata a hukumar ta hanyar yi wa mai girma shugaban kasa yakin neman zabe, duk da cewa ya san hakan ya saba ka’idar aikin hukumar. Hakan fa duk neman gindin zama ya ke a wajen mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari. Sai dai kuma kash! wannan lokacin bai zama daidai da na gwamnatotin ‘yan kama karya ba. Sabo da haka wannan ya jawo masa fadawa cikin damuwa, rudewa ga fitinar da ko ya boye kudi za ta hana shi kaiwa ga muradinsa na neman zama Gwamnan jihar Kano bayan ya yi kicibus da kudaden makarantu.
Wani abu guda da zan so jama’a su gane shine, shi Dakta Bichi ya manta cewa ‘yan Nijeriya masu hankali ne da su ke iya rarrabe magana kuma sun gano cewa tabarmar kunya yake nadewa muraran. Sabo da dukkanin ‘yan Nijeriya suna shaidawa cewa minista malam Adamu Adamu daya ne cikin daidaikun ‘yan Nijeriya da suka yiwa duniya saki uku, suka guji dukkan kayan kyala-kyalenta. Kuma wannan ne ya kai shi ga kololuwar daraja. Dama Dakta ya ko yi wannan a dan lokacin da suka yi da yanzu bai yi nadama ba. ‘Yan Nijeriya ba za su yarda bayan ka tabka musu tilin laifuka ka rika kokarin canja tunaninsu da batun banbancin akida ba, domin ba akida ce ta koya maka mummunan aikin da yanzu ya jefaka nadama ba.
A karshe ina mai shaidawa Dakta Baffa Bichi a kashin kaina zan kalubalance ka gaban babbar kutu a kan kazafin da ka yiwa mutanen da kasa ba ta da irinsu da yawa, kuma sun shirya su bautawa jama’a. Kuma na yanke wannan shawarar ne sabo kaunar da na ke yiwa kasata da ci gabanta. Duk wanda ya san Malam Adamu Adamu ya san shi daya ne cikin ire-iren wadannan mutanen kuma kai ma da kan ka kasan haka sabo da haka ka shirya kare kan ka a gaban kuliya, ina nan kasa mai tsarki zan yi waya da Lauya ya shirya takardu domin zawa kotu.