Musa Muhammad" />

Kalaman Cusa Kiyayya Da Tasirinsu A Tsakanin Jama’a

08148507210   mahawayi2013@gmail.com

A wannan makon, mun dan koma baya kadan don mu yi maimaicin wani rubutu da muka taba yi mai matukar muhimmanci, wanda kuma yake da matukar bukatar da a yi dubi zuwa gare shi don kiyayewa.  Wannan kuwa ba wani ba ne illa batun nan na yadda wasu kan saki bakinsu wajen furta duk abin da ya fito, ba tare da tunanin matsalar da zai iya kawowa ba.

Kowane mutum da Allah ya yi, ya yi shi da irin nasa tunanin, kowa da yadda yake kallon abu idan ya zo masa, kamar yadda yake kuma kowa da irin nasa ra’ayin. Wasu ana iya kawar da su daga kan ra’ayinsa mummuna ko kyakkyawa, wasu kum ba yadda za a yi a iya kawar da su daga ra’ayin da suka ginu a kai.

Irin wannan ra’ayi da fahimta da Allah ya yi kowa tasa daban, shi ne ya kamata a ce kowa ya tsaya a kan nasa, kada wani ya ce dole sai kowa ya bar nasa ya dawo nasa. Idan kowa ya rike nasa, to ba yadda za a a ce an samu wata hatsaniya game da fahimtar wani. Kamar yadda karin maganar Hausawa ke cewa ‘Duniya Zaman Dan Marina, Kowa Da Inda Ya Sa Gabansa!’

A irin wannan yanayi ne ya zama sai ka taras da wani ko wasu suna furta kalaman da za su kawo rudani da wani, wani lokaci ma har yakan kai ga jawo tashin hankali a tsakanin jama’a. Duk irin wadannan abubuwa, ba wani abu ke jawo su ba illa rashin girmama addini, fahimta, kabila ko martabar wani, wanda hakan kuma ke zama babbar barazana ga zaman lafiyar al’umma. Domin wajibi ne, muddun ana tare, to a girmama juna.

Kalaman cusa kiyayya, ko kalaman batanci, dukkansu abu daya ne, domin ba abin da suke jawowa illa rarraba da tashin hankali a tsakanin jama’a. Wasu lokulata ma, abin takaici zaka taras da irin wadannan kalaman suna fitowa ne daga bakin shugabannin addini, wadanda suka hada da Malamai da Fastoci, wanda maimakon su zama masu hada kan al’umma, sai ya zama sun zama masu rabawa, ta yadda za ka ga wasu shugabannin addinin sun bar koyarwar addinin nasu sun koma suna bin ra’ayin kansu, kuma da haka suke jan magoya bayana.

Haka kuma ko ma a cikin addinin, mutum zai taras da cewa ya-su ya-su ma suna cusa irin wannan kiyayya ta hanyar furta kalaman bantanci da cusa kiyayya ga mabiyansu na sauran al’ummar da suke da bambancin fahimta kom ra’ayi da su, inda a wasu lokuta abin har ya kan kai ga zubar da jini. Abin bakin cikin ma wasu lokuta za ka taras da ’yan gida daya ne, amma ba a ga-maciji da juna

Baya ga addini, wani bangare kuma da ake amfani da irin wadannan kalamai na cusa kiyayya a tsakanin al’umma, shi ne bangaren siyasa, wanda za a iya cewa kamar abin ya fi muni ta nan. Domin za ka ga dan siyasa ya dage yana ta furta kalamai na batanci, wanda zai cusa mummanar kiyayya idan abokin hamayyarsa ya ji, wanda ta haka sai ya a ginu a cikin kiyayya da gaba.

Baya ga fannonin addini da siyasa, hatta a tsakanin jama’a ma akwai lokutan da wasu jama’a za su rinka furta irin wadannan kalamai na cusa kiyayya da batanci, wasu lokuta kawai don su haddasa gaba da kiyayya, ko kuma don cimma wata manufa tasu ta kashin kansu. Ta yadda za ka ga wasu lokuta ko a cikin hira ma sai kawai ka ji mutum ya soka wa dan uwansa wata magana, wanda in ba hankali aka yi ba, nan da nan sai a tashi da tsiya.

Duk idan muka bi wadannan fannoni na addini, siyasa da zamantakewa, za mu ga cewa babu bukatar a rinka tofa, ko furta irin wadannan kalamai. Domin a har kullum babu wani abu da suke haifarwa, kamar yadda na fada a sama, illa gaba da kiyayya, wasu lokuta ma har ta kai ga zubar da jini, wanda idan da an bi abin da ya dace, to hakan ba za ta faru ba.

A na samun sabanin ra’ayi tsakanin Kalaman Cusa Kiyayya da kuma Hakkin Furta Albarkacin Baki. Wadannan abubuwa guda biyu suna da bambanci sosai a tsakaninsu. Furta Albarkacin Baki, wata dama ce da mutum ke da ita na fadin ra’ayinsa game da wani, ko wasu ko shugabanninsa, wadanda yake ganin idan fada kila a gyara, ko kuma ya fahimtar da wasu game da abin da yake fadi. Amma ba zai zama ya yi amfani da wannan dama don zagi ko jawo gaba da kiyayya ba.

Sannan Kalaman Cusa Kiyayya, wadannan a bayyane suke, wato kalamai ne da mutane kan yi don kawai su jawo kiyayya da tsana a tsakanin jama’a. Da irin wannan wasu ke ganin cewa wai idan an hana su furta wasu kalamai, ko an kama su don sun yi haka, sai su rinka ganin tamkar an tauye masu hakki ne fadin albarkacin baki, musamman a tsarin mulki irin na dimokradiyya.

Akwai wani lokaci da Shugaban Majalisar wakilai ta Nijeriya, Hon. Yakubu Dogara ya taba furta wata magana game da wannan maudu’i namu, inda ya ce “ita dimokradiyya ta gaji surutu, amma tana dauke ne da surutan da za su jawo tattaunawa, ba surutan da za su jawo rikici ba. Duk lokacin da wasu kalamai ko surutai suka jawo tattaunawa a tsakanin jama’a, to wannan ya zama surutu mai lasisi. Amma duk lokacin wasu surutai ko kalamai suka jawo tashin hankali, to sun zama kalaman batanci, kuma kalaman batanci ba su da wurin zama a dimokradiyya.”

Ina ganin wadannan kalamai na Yakubu Dogara, kalamai ne da ba sa neman wani karin bayani balle fassara, domin ya fayyace bambancin da ke tsakanin kalaman da suka dace da sunan furta albarkacin baki da kalaman da za su cusa gaba da kiyayya a tsakanin jama’a, balle mutum ya fake da dimokradiyya ya ci zarafin wani.

Wannan ne ya sa nake ganin gwamnatin Nigeriya, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta cancanci yabo wajen dokar da ta kafa na haramta furta irin wadannan kalamai na cusa kiyayya a tsakanin jama’a, inda musamman ta fi mayar da hankali wajen jan kunnen kafafen yada labarai, musamman rediyo da talbijin. Domin ta kafafen yada labaran ne irin wadannan mutane ke samun daman baje klinsu.

Irin wadannan kalamai, gwamnatin na daukarsu a matsayin daya daga cikin manyan laifuka, wadanda idan aka kama mutum yana yinsu, to tamkar ya aikata wani laifi ne da ya shafi ta’addanci, domin shi ma abu ne da ke kai ga zubar da jinin jama’a.

A kwanakin baya, lokacin da Ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad ke gabatar da wani jawabi, ya bayyana cewa gwamnati ta umurci Hukumar kula da kafafofin yada labarai ta NBC ta hukunta duk wani gidan rediyon da aka samu ya ba wani dama yana furta irin wadannan kalamai da ka iya kawo tashin hankali ko kiyayya a tsakanin jama’a.

Alhaji Lai ya ce, wasu lokuta idan mutum ya bude rediyo zai yi mamakin jin irin abubuwan da ke fita daga bakunan wasu jama’a, inda a lokuta da dama wasu ke ganin suna yin haka ne da sunan siyasa, wanda shi kuma yana ganin ba abin da wannan abu zai kawo illa fitina.

Za mu kwana a nan. A makon gobe in Allah ya yarda za mu ci gaba da bayani game da yadda gwamnatin ta dauki wannan abu, sannan da yadda wasu masana a harkar Shari’a suke kallon abin.

 

Exit mobile version