A ranar Jumma’a 12 ga watan Janairu 2024 ne kotun koli ta yanke hukuncin karshe a kan takaddamar da taso tun daga tokun sauraron kararrakin zaben gwamnoni a jihohin da suka hada da Legas, Kano, Bauchi, Filato da Zamfara inda kotun ta tabbatar da zaben da al’umma suka yi wa gwamnonin wadannan jihohin.
Ganin irin gwagwarmayar da aka yi fama da ita da yadda kan al’umma ya rarrabu, ya sa mutane da dama ke ganin akwai kalubalen da gwamnonin ke fuskanta a halin yanzu na hada kan al’umma ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
- Kasar Sin Ta Harba Kumbon Dakon Kaya Domin Aikewa Da Kayayyaki Ga Tashar Sararin Samaniya
- ‘Yansanda Sun Cafke Wasu Mutane Biyu Da Ake Zargi Da Satar Keke-napep A Kano
Musamman a halin yanzu da ya kamata a fuskanci yi wa al’umma aiki, ganin mutane na fuskantar matsalolin tattalin arziki daban-daban da kuma matsaloilin tsaro da ke bukatar kulawa cikin gaggawa.
Kotun kolin ta yanke hukunci a kan zaben Babajide Sanwo-Olu na Legas, Abba Yusuf na Kano, Bala Mohammed na Bauchi, Caleb Mutfwang na Filato da kuma Dauda Lawal na Zamfara inda ta tabbatar da su a matsayin gwamnonin jihohinsu wanda hakan ya kawo karshen takaddamar da ke tattare da zaben gwamnonin da aka yi a shekarar 2023.
Kano
Batun Rusau Da Hada Kan Jam’iyya Ne A Kan Gaba
Akwai yiwuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf zai fuskanci manyan kalubale da suka hada da rikicin cikin gida wanda tun kafin a ci Talata da Laraba aka fara jin karar tasowarsa, wadannan kuma ba ya rasa nasaba da yadda wasu daga cikin masu taimaka wa gwamnan da kuma wasu kwamishinonin suke karbar umrnin daga babbar fadar Jam’iyyar ta NNPP, domin kamar yadda aka sani Gwamana Abba kafin wannan lokaci, shi ne mai taimakawa na musamman (PA) na Sanata Kwankwaso, hakan ta sa wasu dagan cikin masu rike da manyan mukamai har yanzu suke masa kallon PA.
Hakazalika, akwai gagarumar matsalaar da ta kamata tun yanzu Gwamna Abba ya fara tunanin yadda zai magance ta rusau da aka yi wa ‘yan kasuwa da wasu daidaikun mutane a Birinin Kano.
Wannan ba karamin kalubale ba ne idan aka yi la’akari da kasancewar Kano cibiyar ciniki kuma ga shi kai tsaye ‘yan kasuwar aka fara tabawa. Sai kuma batun korar ma’aikata wadda a wata majiya ta shaida cewa wannan matsala ce da ta tayar da matukar kura da ake ganin ita ce ta kai wani babban jami’in gwamnatin tafiya jinya a asibiti, kodayake an sallamo shi.
Hakazalika, akwai batun masarautu hudu da tsohon Gwamna Ganduje ya kirkira, kuma ake ganin suna cikin abubuwan da ba su kwanta wa wannan gwamnati a zuciya ba, sannan suna da tsarin abubuwan da suka ambata a lokacin yakin neman zaben da dole su aiwatar da su, kamar batun kawar da gine-ginen da suka ce ba a yi su bisa ka’ida ba kuma suka yi masu dirar mikiya. Ko shakka babu akwai bukatar sabon gwamnan ya yi wa wannan matsala kallon tsanaki domin gudun sake fadawa wani rikicin.
Ganin yadda Kanawa suka nuna wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kauna ya zama wajibi ya duba wasu daga cikin abubuwan da za su kara kyautata alakar gwmanatinsa da wasu sassan da suke ganin an saba masu a baya, kuma kamar yadda aka san al’adar siyasar Jihar Kano, akwai wasu rukunin al’umma kama da ga ‘yan Kasuwa, Malamai, iyayen kasa da masu fada aji daga cikin ‘yan siyasa da suke taka muhimmiyar rawa wajen nuna kyakkyawar alkiblar kowacce gwmanati, wannan tasa yake da muhimmacnin gaske gwamnan ya gaggauta yin la’akari da su domin taimaka wa gwamnatinsa. Duk da cewa dai jim kadan da yanke hukuncin kotun koli aka ji gwamnan ya sanar da kafa wani Kwamitin Dattijai da ya kunshi Tsoffin Gwmanonin Jihar Kano guda uku da suka hada da Malam Ibrahim Shekarau, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Zamfara
Mastalar Tsaro Da Bukatar Hada Kan Al’ummar Jihar
A yanzu haka hankalin Gwamna Dauda Lawal ya kwanta sakamakon tabbatar da shi da Babar Kotun Koli ta yi na cewa, shi ne zabben gwamna.
Daga kalubalen da Gwamna Dauda zai fuskanta, akwai daga bangaren ma’aikata,’yan siyasa da al’ummar gari-gari.
LEADERSHIP Hausa ta ji ra’yoyin mazauna Zamfara, kuma masana a kan zamantakeyar yadda Gwamna Dauda zai magance wadannan kalubalen da ke gabansa.
Kwamaret Ibrahim Kanoma Tsohon Ma’aikaci a Ma’aikatar yada labarai na Zamfara, ya bayyana cewa, babban kalubalen da ke gaban gwamna a bangaren ma’aikata shi ne dawo da darajar aikin.
Bangaren Siyasa kuma Malam Ibrahim Gada ya bayyana cewa, babban kalubalan Gwamna Dauda shi ne, Sanata Yari Abubakar, dan yadda a yanzu yake tafiyar da ‘yan siyasa da ba su tallafi da taimakonsu, lallai shi ma Gwamna Dauda sai ya kasance haka, tun da ga aiki yana ta zubawa sai kuma alheri ga ‘yan siyasa don yadda ake cikin yanayi a yanzu haka duk ayyukan da Gwamna Dauda zai yi idan bai hada da tallafin kudi da abinci ba lallai akwai matsala.
Don haka Gwamna Dauda ya duba da kyau ya bullo da wasu shiri na ba da tallafi ga al’umma don rage radadin halin da ake ciki, in ji shi.
Filato
Matsalar Tsaro Ita Ce Babbar Kalubalen Da Gwamnan Jihar Ke Fuskanta
Bayan tabbatar da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, a matsayin gwamnan jihar ba kamar yadda kotun daukaka karar ta yi na dora dan takarar jam’iyyar APC, Nentawe Goshwe ba, babban kalubalen da yake fuskanta shi ne rashin tsaro wanda hare-haren da aka kai wa wasu al’ummomi lokacin bukukuwan kirsemeti suka fayyace irin matsalar tsaron da jihar ke ciki.
Baya ga sha’anin tsaro, ta fuskar siyasa ma Gwamna Caleb na fuskantar kalubalen hada kai da ‘yan majalisa da suka fito daga jihar wadanda suka fi yawa a jam’iyyar dawa ta APC a jihar. Dole Gwamnan ya samar da hanyoyin kara fahimtar juna da mutunta juna a tsakanin al’ummar jihar in har ana son samun ci gaba mai dorewa ci gaba da zamantakewa a jihar.