Kamfanin siminti na Dangote da kuma na BUA sun sanar da cewar, zasu dauki sabbin ma’aikata a wannan zangon.
Abdussamad Rabiu shi ne shugaban Kamfanin na BUA da kuma shugaban rukunonin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote sun ne suka sanar da neman ma’aikatan a shafinsu na sada zumunta na Facebook a daren ranar Talatar data gabata.
Shugabanin sun sanar da cewa,duk mai bukatar yin aiki da su, ya garzaya shafinsu na yanar gizo-gizo.