Kamfanin gine-gine na kasar wato CCECC, ya kaddamar da ginin wani titin mota da zai rage cunkoso a birnin Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya.
An kaddamar da aikin, wanda aka yiwa lakabi da “Collector Road C01” a ranar Jumma’a, kuma hukumar gudanarwar birnin Abuja ta ayyana sabon titin da za a gina a matsayin aikin gaggawa, wanda aka tsara kamfanin na CCECC zai kammala cikin watanni shida.
Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, ministan birnin Abuja Nyesom Wike, ya ce aikin na da matukar muhimmanci, zai kuma hade sassan gunduma mai kunshe da hukumomi da cibiyoyin bincike, ciki har da babban ginin ofisoshin ma’aikatan shari’a, wanda shi ne matsugunin jami’an fannin shari’a mafi girma a kasar, da kuma yankin cibiyoyin ilimi mafi girma dake birnin. (Saminu Alhassan)