Babban kamfanin fasaha na kasar Sin wato Huawei, ya kaddamar da sabuwar manhajar sa, ta ba da kariya ga na’urorin sassan gwamnatin kasar Kenya da ma sassa masu zaman kan su.
Yayin kaddamar da manhajar mai lakabin “Ransomware Protection 2.0” a jiya Juma’a a birnin Nairobi, fadar mulkin kasar, babban jami’in kamfanin reshen kasar Kenya Gao Fei, ya ce manhajar za ta inganta amfani da runbun adana bayanai, da fasahohin kwaikwayon tunanin bil adama na AI, a gabar da ake kara fuskantar barazanar kutse daga maharan yanar gizo.
Gao Fei, ya kara da cewa, sabuwar fasahar, ta tabbatar da muhimmancin bukatar da ake da ita, ta samar da kariya mai nagarta, a gabar da Kenya ke kara cin gajiya daga fasahohin sadarwa na zamani.
A nasa bangare kuwa, babban jami’in ayyukan fasahar kare bayanai na Data, a kamfanin na Huawei reshen kasar Kenya Naveen Kumar, cewa ya yi sabuwar manhajar da suka gabatar, tana samar da bayanai na kai tsaye, na sa ido da ba da kariya daga hare-haren yanar gizo. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)