Kamfanin Kasar Amurka Zai Horas Da Matasa 300 A Kan Makamashin Hasken Rana A Jihar Kebbi

Daga Umar Faruk Birnin,

Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shiri da kamfanin kasar Amurka domin horas da matasa sama da 300 a kan makamashin hasken rana.

Kwamishinan ayyuka na musamman Barista Attairu Maccido ya tabbatar da haka a yayin bikin kaddamar da horon ga matasan mata da aka zabo guda dari da hamsi kafin isowar turanwan kamfanin na Amurka Jihar.

Barista Maccido, ya bayyana cewa, matasan da aka zabo sun hada da mata 150 da maza 150 kuma za a ba su horo na tsawon makonni 10 a karkashin kulawar kamfanin kasar Amurka wanda za a fara nan da watan Fabrairu.

Maccido ya kuma kara da cewa, horon cikin gida da gwamnatin jihar ta fara a yanzu tare da ‘yan mata 150, zai fara aiki har zuwa watan Fabrairun 2022 yayin da kamfanin na Amurka zai fara aiki a watan Fabrairu zai kasance na tsawon makonni goma.

Tun da farko, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin wutar lantarki, Alhaji Yusuf Haruna Rasheed ya bukaci mahalarta taron da su sadaukar da kansu ga wannan horon, yana mai cewa horo ne da ya cancanci kwazo da maida hankali.

A cewarsa, “A matsayinmu na mata, muna ganin ya zama dole mu fara da ku ad ku ne ginshikin al’umma, a lokacin da mata suka kasance masu hazaka kuma suke ba da gudummawa ga ci gaban al’umma, tabbas, sararin sama shine iyaka ga wannan al’umma har zuwa yanzu. kamar yadda ci gaba ya damu, “in ji shi.

Haruna-Rasheed ya bukaci su da su yi amfani da wannan damar domin samun ci gaba a rayuwarsu da kuma ci gaban iyalansu.

A nasa jawabin, daya daga cikin masu horaswar Umar Faruku, ya godewa gwamnatin jiha bisa daukar nauyinsu na halartar horo da dama akan wutar lantarki da hasken rana a cibiyar horas da matasa ta kasa NAPIN.

Ya ce, horon ya ba su damar kara sanin wutar lantarki da makamashin hasken rana, inda ya ba su tabbacin cewa, za su ba da ilimi iri daya ga matasa a cikin al’umma.

Exit mobile version