Shugaban kasar Kenya William Ruto, ya jagoranci bikin kaddamar da aikin karewa, da farfado da kogin Nairobi na kasar ta Kenya.
Bikin kaddamar da aikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin Kenya, da jagororin kamfanin Energy China da zai gudanar da kason farko na aikin, da masu rajin kare muhalli. Ana kuma sa ran zai dawo da kyakkyawan yanayin muhallin halittu a kogin Nairobi, musamman ganin yadda kogin ya ratsa babban birnin kasar ta Kenya.
- Bayan Shekaru 115 Manchester United Za Ta Gina Sabon Filin Wasa
- Fashewar Gas Ta Hallaka Yaro, Ta Jikkata Mutum 21 A Kano
Karkashin tsarin aikin, za a samar da rukunin gidaje masu rahusa, zai kuma gudana cikin shekaru 4, yayin da za a kashe kudi har shillings biliyan 50, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 388 wajen aiwatar da shi.
A jawabinsa yayin bikin kaddamar da aikin, shugaba Ruto ya ce farfado da kogin Nairobi bayan shafe gomman shekaru yana a gurbace, zai samar da guraben ayyukan yi ga matasa, da inganta tsarin kiwon lafiya, da kyautata yanayin muhallin birnin.
A watan Fabarairun da ya gabata ne gwamnatin Kenya, ta sanya hannu da kamfanin China Energy, don gudanar da kason farko na aikin, wanda gwamnatin Kenyan ta samar da kudin gudanarwa, aikin da ya kunshi gina manyan magudanan ruwan dagwalo, da cibiyoyin tace ruwa, da na inganta cibiyoyin samar da ruwa, da yashe kogi, da tsumin ruwan da ake killacewa, da tsarin cin gajiya daga bola, da kayata filaye, da samar da gidaje masu rahusa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp