ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kamfanin Sin Ya Haskaka Kauyen Lauteye Na Jihar Kanon Nijeriya

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Hasken lantarki, muhimmin bangare ne na ababen more rayuwar dan Adam, musammam a wannan zamani da muke ciki da komai ke da alaka da hasken lantarki.

Tsayayyen wutar lantarki ko akasinsa, wani mizani ne na auna ci gaban wuri. Don haka, samun wutar lantarki daga makamashi mai tsafta, wani karin tagomashi ne ga rayuwar bil adama da muhalli.

  • Yawan Jarin Da Sin Ta Zuba Kai Tsaye A Ketare Ya Kai Matsayin Gaba Na Uku A Duniya Cikin Jerin Shekaru Goma Da Suka Wuce

Na yi wannan shimfida ne bisa la’akari da gagarumar gudunmawar da kamfanin PowerChina ya bayar a baya-bayan nan, inda ya gwangwaje kauyen Lauteye na yankin karamar hukumar Bunkure ta jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya, da na’urori 500 na samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana.

ADVERTISEMENT

Samun wannan labari, ya yi matukar faranta min rai, ganin yadda wani mutumin yankin mai shekaru sama da 40, ya ce kauyen nasu bai taba samun hasken lantarki ba.

Sin

LABARAI MASU NASABA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

Hakika wannan yunkuri na kamfanin kasar Sin zai taimakawa al’ummar kauyen, ta hanyoyi daban-daban. Misali, za a samu ingantuwar tsaro, harkokin kasuwanci za su bunkasa, dalibai za su kara samun damar bitar karatunsu, al’umma za su samu damar more fasahohin zamani, kana za su daina kashe kudin sayen gawayi ko kalanzir ko kyandir da sauransu, haka kuma, ina da yakinin ya bude wa kauyen wani sabon babi na ci gaba.

Yunkurin wani bangare ne na shirin kamfanoni 100 a kauyuka 1,000, wanda kungiyar ’yan kasuwar kasar Sin a Afrika ta kirkiro, da nufin tattara kamfanoni kasar Sin 100, domin su aiwatar da ayyuka 1,000 da al’ummomin nahiyar za su ci gajiyarsu.

Baya ga taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin nahiyar da samar da guraben ayyukan yi da gudanar da ayyukan agaji, kamfanonin kasar Sin suna kokarin tallafawa al’ummomin kauyuka da ba kowa ne zai tuna da su ba.

Shi ya sa a kullum na kan ce, kasar tana da hangen nesa da sanin ya kamata, domin na tabbata, mutanen kauyen da ma jihar Kano, har da kasarmu ba za su manta da irin taimakon da Sin ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow
Daga Birnin Sin

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Fara Aiki Da Na’urar Fasahar Samar Da Lantarki Daga Iskar CO₂ Da Aka Sarrafa A Lardin Guizhou Na Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Mutum 4 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wani Abu A Babbar Kasuwar Onitsha

Mutum 4 Sun Mutu Sakamakon Fashewar Wani Abu A Babbar Kasuwar Onitsha

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.