Kamfanonin Waje Na Neman Kulla Kasuwancin Mai Da Matatar Dangote

Dangote

Daga Mahdi M. Muhammad

Rukunin Kamfanonin Dangote, babbar masana’anta a Nijeriya da hamshakin mai kudin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya kafa, ta bayyana cewa, manyan kamfanonin mai daga gabas ta tsakiya da kasashen yamma sun nemi kulla yarjejeniyar samar da danyen mai da matatar Dangote.

Kamfanin hadin gwiwar, ya kuma tabbatar da wani rahoto da manema labarai suka gabatar a ranar Juma’a cewa, Kamfanin mai na kasa (NNPC) ya nemi mallakar kaso 20% na matatar mai na ‘Reuters’.

Babban darakta na dabarar kayayyaki, fasahohi da tattalin arziki a Masana’antun Dangote, Mista Debakumar Edwin ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Kamar yadda aka nuna a cikin rahoton na Reuters, Edwin ya bayyana cewa, akalla kamfanonin mai hudu, ciki har da kamfanin mai na kasar ya tuntube shi don sayen kadarar.

Edwin ya bayyana cewa, kamfanonin man daga kasashen Yamma da na Gabas ta tsakiya wadanda suke kasuwanci da samar da danyen mai suna kokarin kulla yarjejeniyar samar da danyen mai, makamancin wannan manufar ta NNPC.

Rahoton ya lissafa Bitol, wani kamfanin samar da wutar lantarki da sayar da kayayyaki na kasar Holan da Trafigura, wani dan kasuwar kasar ta Singapore dan kasuwannin kayayyaki da yawa daga cikin kamfanonin da ke neman yarjejeniyar samar da danyen mai ga matatar.

An ruwaito Edwin yana cewa, kamfanonin mai suna neman samun kaso 20% na marasa karfi a matatar Dangote a wani bangare na hadin gwiwa ta yadda za su sayar da danyen mai.

Ya ce, matatar Dangote ba ta neman daidaito kuma kamfanin na son samun damar danyen mai daga kasuwa. Nijeriya, babbar kasar da ta fi fitar da danyen mai a Afirka, tana shigo da kusan dukkanin mai saboda matatun mai na jihar, wanda hakan ya sa kamfanin mai na jihar ke sha’awar 650,000 na matatar mai ta Dangote a kowace rana.

“Nijeriya ta rasa babbar kwastomomin ta, Amurka, bayan ta fara samar da man ake kira shale. Amurka yanzu haka tana matsawa zuwa wasu kasuwannin da suka fi daraja a Nijeriya,” in ji Edwin.

A cewarsa, an shirya kammala matatar a bana tare da fara aiki a watan Janairun 2022.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa, NNPC ta bayyana aniyarta ta sayen kaso 20 na marasa rinjaye a matatar Dangote.

Matatar, ana sa ran za ta sarrafa nau’ikan haske da matsakaita na danyen mai, ciki har da fetur da dizal da man jirgin sama da polypropylene, mallakar kamfanin Dangote ne na Nijeriya kuma ya kai kimanin dala biliyan 15.

An tsara shi don samar da lita miliyan 50 na man fetur da lita miliyan 15 na dizal a rana, kimanin tan miliyan 10.4 na samfurin, tan miliyan 4.6 na diesel, da tan miliyan 4 na man jirgin sama a shekara, ban da samun takin zamani, wanda zai yi amfani da matatar mai ta kayan aiki a matsayin kayan aiki.

Da yake magana a yayin bikin baje kolin damar samun mai da Gas na Nijeriya (NOGOF), a shekarar 2021, mai taken, ‘Bayar da damar da hadin kai don dawo da yaduwar mai na masana’antar mai da iskar gas ta Nijeriya,’ Babban Jami’in gudanar da ayyuka na kamfanin, matatar mai da albarkatun mai, Mustapha Yakubu, ya ce, tattaunawa ta riga ta gudana don hakan.

Babban jami’in kamfanin na NNPC ya bayyana a yayin taron cewa, hadin gwiwar zai kara tabbatar da samar da kayayyaki ga ‘yan Nijeriya ba tare da wata matsala ba yayin da yarjejeniyar ta fara aiki, yana mai lura da cewa daya daga cikin bangarorin na ta, kamar, ‘Greenfield Refining Projects Dibision’ (GRPD) tana kula da batutuwan da suka shafi kammala yarjejeniyar.

“Muna da abin da muke kira koren matatun mai, da kuma ‘Greenfield Refining Projects Dibision’ (GRPD) na NNPC. Abin da muke yi, dabarunmu shine hadin kai da neman hadin gwiwa tare da masu saka hannun jari. A yanzu haka, muna da matatar Dangote wacce take da ganga dubu 650,000 a kowace rana gami da karamar tan 80,000 a kowace shekara,” in ji shi.

Y ace, “me muke yi a can? zan iya fada maku a yau cewa muna neman samun kaso 20 cikin dari na kaso mai tsoka a matatar Dangote a matsayin wani bangare na hadin gwiwarmu, kuma kun san cewa akwai tarin danyen mai da yawa a wannan matatar. Wannan ganga 650,000 kenan, za a shiga guda daya daga cikin daskare danyen mai (CDU). Lokacin da wannan ya hau, to shi ma zai shayar da mu kasar baki daya.”

Exit mobile version