Kana Da Sha’awar Kiwon Salwa?

Salwa

Daga Abubakar Abba

Kiwata Salwa na da matukar mahimmanci, domin namanta da kuma kwanta, ana da matukar bukatarsu, saboda idan kana da matan Salwa guda 600, za ka iya samun akalla kwai 11,000 a cikin kowane wata daya.

1 Jari: Ya zama wajibi ka kasance kana da jari kafin ka fara kiwata Salwa, musammna domin ka samu cin nasara a kasuwancinka.

2 Samar Da Wajen Kiwata Ta:

Ya kamata ka samar da wajen da ya dace domin kiwata ta, musamman wajen ya kasance waje ne da suka fi bukata.

3 Tanadar Kayan Kiwata Ta:

Ya kamata ka tabbatar da ka mallaki kayan da suka dace na kiwata, musamman kayan ba su ruwansha da kayan zuba muta abinci da kuma ida za ta dinga saka kwanta.

4 Ciyar Da Ita Abinci:

Yana da kyau ka ciyar da ita abinci yadda ya dace, duk da cewa, basu cika damuwa da cin abinci ba mai yawa ba.

5 Tanadar Mata Da Magunguna:

Yana da kyau, ka tanadar mata da magunguna da za a dinga ba ta yayin da suka kamu da wata cuta.

 

6 Kasuwancinta:

Yana da kyau, ka sanar da abokan cinikinka, ka sanar da su cewa ka kiwata Salwar don su saya, za ka kuma iya kai ta gidajen sayar da abinci ko Otel-otel don sayarwa ko kuma ka kai kasuwa.

Shin Ana Samun Riba A Kiwon Salwa?

Tabbas ana samun riba mai dimbin yawa daga kiwon tsintsun Salwa, amma kafin ka fara kiwata Salwa, ana son ka tabbatar da ka yi tsarin kasafin kudaden da za ka kashe wajen kiwata ta, haka kuma, kiwata Salwa ba sai ka zuba wani jari mai yawa ba domin za ka iya farawa da ‘yan kudi kadan don kiawata ta.

Tsawon Wanne Lokaci Salwa Take Kai Wa Kafin Ta Girma?

Tana da saurin yin girma kuma ta kasanace daya daga cikin tsintaye masu saurin yin girma, inda daga lokacin da ta fara yin kwanta har zuwa girmanta, tana kai wa sati shida, inda kuma daga sati tara zuwa sha biyu, za a iya cin namanta.

Sai dai, wasu sun fi fara cin namata daga watanni tara zuwa sha biyu.

Shin Sau Nawa Ne Yakamata A Ba Ta Abnici?

A kowace safiya yakamata a tanadar mata da wadataccen abinci, haka ana son a kodayaushe, ta kasanace an tanadar mata da abinci.

Amfani  Takwas Da Za A Samu A Kiwata Salawa Don Kasuwanci:

Kiwonta na kara zama sananne abu, yau da kullum domin tana da matukara amfani, kuma fanni ne da za ka iya samun karin kudin shiga kan lokaci.

Salwa na samar da nama da kuma kwai, musamman ganin cewa, ana da yawan bukatar naman da kuma kwan a kasuwanni.

Amfanin Kiwata Salawa:

Ba su da wuyar kiwatawa, domin yawancinsu, kananan ne kuma ba su cika bukata ba, sai ana ba su kulawa ta musamman.

Tana Tafiyar Da Kasauanci:

Salwa na kara tafiyar da kasuwanci yadda ya kamata kuma tana samar da kudi ga wanda ya rungumi kiwonta.

A ka’ida, Salwa na kammala yin girmanta ne daga sati shida, inda kuma ta ke fara yin kwai daga sati shida, inda za ka iya fara sayar da wasu daga cikin kwanta don samun kudin shiga.

Kula Da Ita:

Salwa bata cika bukatar wata kula wa ba, domin tsintsaye ne yan kanana kuma basu cika buktar sararin wajen da za su dinga wataya ba.

Salwa Ba Ta Cika Bukatar Abinci Mai Ywa Ba:

Ba ta cika yawan bukatar abinci ba, idan aka kwatanta da sauran tsintsayen da ake kiwatawa don kasuwanci ba.

 

Cutuutuka Ba Su Cika Harbin Salwa Ba:

Salwa cututtuka ba su cika harbin ta ba, sabanin sauran tsitsayen da ake kiwata wa don kasuwanci haka, bata cika yawan yin rashin lafiya ba.

Ana Da Yawan Bukatar Namanta:

Mutane na da wayan bukatar naman Salawa a kasuwanni har kuma da kwanta, musamman ganin tana dauke da sinadarin fat da na protein. Haka naman tana taimakwa wajen yin maganin cututuuka kamar su hawan jinni, tarin fuka, ciwon suga da sauransu.

Ribar Da Ake Samu Wajen Kiwata Salwa:

A kalla ana sayar da kwanta kan farashi mai yawa kuma tana saka kwai a kullum haka, iya girman kwanta iya farashin sa.

 

Exit mobile version