Hukumar masana’antu da sadarwa ta kasar Sin ta ba da alkaluma cewa, daga watan Janairu zuwa Agusta na bana, kanana da matsakaitan kamfanonin Sin sun samu bunkasuwa mai dorewa, inda kudin shigarsu ya samu kyautatuwa, kuzarin kasuwanni ya samu ingantuwa filla filla.
A cikin wadannan lokuta, yawan ribar da sana’o’i 19 na wadannan kamfanoni suka samu ya ci gaba da karuwa, daga cikinsu yawan karuwar sana’ar kera motoci da masaka ya kai kashi 34.2% da 18.7%.
- Xi Jinping Ya Gana Da Mahalarta Taron Sada Zumunta Tsakanin Sin Da Ketare
- Janar Gowon: Tsohon Shugaban Kasa Mafi Tsawon Rai A Nijeriya Na Cika Shekara 90
Ban da wannan kuma, yawan wutar lantarki da kanana da matsakaitan kamfanonin dake da fifiko a wasu bangarori ya karu da kashi 7.9% da 5%, lamarin da ya bayyana farfadowar ayyukansu.
A bangaren ciniki, wadannan kamfanoni na amfani da zarafin farfadowar cinikin duniya, suna kokarin habaka kasuwannin ketare bisa cinikin kasa da kasa ta yanar gizo da sauransu, hakan ya sa cinikin fitar da kayayyaki zuwa ketare ke tafiya cikin karko da samun bunkasuwa yadda ya kamata. (Amina Xu)