KANNYWOOD: Zaki Bari, Damisa Bari… Yadda Rigimar Afakallahu Da Officer Ta Janyo Baraka Kan Korar Rahama Sadau

Da yawan masu kallon finafinan Hausa da bibiyar abubuwan da ke faruwa a masana’antar shirin fim ta Kannywood na dauka cewa, haka-siddan a ke ta faman kwan-gaba-kwan-baya kan korar Jaruma Rahama Sadau daga masana’antar, inda a yayin da hukumar tace finafinai ta Kano ke cewa za ta cigaba da duba finafinan jarumar, ita kuma kungiyar masu shirya finafinai ta ke cewa ba ta san zancen ba.

To, amma bayanai sun tabbatar da cewa, ba haka kurum a ke samun ja’injar ba, domin lamarin ba zai rasa nasaba da wani sabani da a ka samu tsakanin Babban Sakataren hukumar tace finafinai da dab’i ta jihar Kano, Malam Isma’il Na’abba (wanda a ka fi sani da Afakallahu) da sakataren hadaddiyar kungiyar masu shirya finafinai ta kasa, MOPPAN, reshen jihar Kano, Malam Salisu Muhammad (wanda a ka fi sani da Officer), ba.

Wata majiya mai tushe a cikin masana’antar Kannywood ta tabbatar da cewa, kace-nacen da a ke yi ba shi da nasaba kwata-kwata da korar Jaruma Rahama Sadau, illa dai kawai a na yin amfani da hakan ne a matsayin wata mafaka da za a fake da ita wajen muzguna wa juna.

Binciken wakilinmu a Kano ya tabbatar da cewa, ba a samu baraka da rarrabwar kai kan korar Jaruma Sadau ba har sai bayan da wadannan jiga-jigai guda biyu, wadanda aminan juna ne a baya, su ka raba gari a kan aikin kwamitin yaki da masu satar fasahar finafinai.

Majiyar wakilinmu ta nuna cewa, lamarin ya samo asali ne kan wata wasika da Afakallahu ya aike wa MOPPAN ta Kano, wacce a ciki ya bayar da umarnin dakatar ya yaki da satar fasaha a fadin jihar har sai bayan hukumarsa ta kammala tsare-tsarenta, lamarin da ya fusata Officer, inda a matsayinsa na sakataren kungiyar ta masu sana’ar shirin fim ya ke zargin Afakallahu da yin zagon kasa ga mambobinsa.

Majiyar ta cigaba da cewa, a daya bangaren kuma a na kyautata zaton Afakallahu ya na zargin kwamitin da amsar makudan kudade daga masu satar fasahar da a ke kamowa ba tare da bai wa bangarensa kason komai ba; lamarin da ’yan kwamitin ke kallo a matsayin sa’ido, kyashi, katsalandan da kwadayi. To, amma ta fuskarsa shi kuma ya na ganin zai taimaka wa masu sana’ar ne ta hanyar samar da wani tsari tsakaninsu da ’yan dawunlodin (wato masu sana’ar kwafar fim su na saka wa a wayoyi da memori kad).

Kin ba shi hadin kai da Salisu Officer ya yi, kamar yadda ya saba ba shi a baya duk lokacin da ya ke da wata bukata kan ’yan fim, a na ganin shi ne ummul’aba’isin samun baraka tsakanin bangarorin biyu, inda ya yi amfani da batun korar Rahama Sadau, don rage wa kungiyar karfin fada-a-aji a cikin masana’antar ta Kannywood duk da cewa kafin hakan ya sha amfani da Officer wajen biyan bukatun siyasar Kannywood a wajen gwamnatin jihar Kano.

Binciken wakilinm ya nuna cewa, ko a lokacin da masu sana’ar shirin fim su ka nemi su yi tawaye kan kama wa da tsare fitaccen mawakin nan, Sadik Zazzabi, da hukumar tace finafinai ta yi kan zargin ya saki wakoki ba bisa ka’ida ba, shi Salisu Officer ne ya rubuta wa gwamnatin jihar takarda ya na mai tabbatar ma ta da goyon bayan masu sana’ar a rubuce; lamarin da ya sage gwiwar masu shirin yin tawayen, shi kuma Afakallah ya samu sassauci daga matsin lamba da barazanar rasa kujerarsa da a ke zargin ta taso.

Duk da cewa, akwai wadanda ba su ji dadin daukar wannan mataki na mara wa Afakallahu baya da Officer ke yi a bay aba, amma sun kasa fitowa fili su bayyana ra’ayinsu, watakila saboda tsoron abinda ka je ya komo, domin karfi da karfi ne su ka hadu; Afakallahu daga bangaren gwamnati, shi kuma Officer daga bangaren kungiya.

Don haka a na samun bullar waccan baraka a tsakanin jiga-jigan guda biyu, sai wasu da ke gefe, wadanda kila da ma gamayyar ta hana su rawar gaban hantsi su ka yi sauri su ka shigo, don sake farraka tsakaninsu.

A na zargin Jarumi Ali Nuhu na da hannu dumu-dumu a cikin lamarin na kawo baraka, domin shi ne ya fara daukar Rahama ya kai ta wajen Afakallahu (wanda a ke ganin ya na neman hanyar da zai rage wa MOPPAN karfi), inda shi kuma shugaban hukumar sai ya rungumi jarumar hannu bibbiyu, duk da cewa a baya din ba ya tare da ita.

A ganin wasu, ba abin mamaki ba ne Jarumi Ali ya nema wa Rahama gafara kan zargin aikata badala da a ke yi ma ta, domin wasu na ganin duk jirgi daya ne ya dauko su, to amma abin mamaki ne ganin yadda Afakallahu ya shiga jerin ’yan gaba-gaban Rahama, domin babu abinda ya hada biri da gada. Wannan ne ya sanya masu zargin Afakallahu ya yi haka ne don kawai ya rage wa kungiyar baya, su ke ganin cewa hasashensu daidai ne.

Faruwar wannan ya nemi ya kawo tasgaro kan hadakar kungiyoyin da ke karkashin MOPPAN, inda bisa umarnin shugaban bangaren kungiyar jarumai, Alasan Kwalle, sai Jarumi Rabiu Rikadawa ya bayar da sanarwar cewa, kungiyar jarumai ta jihar Kano ta na goyon bayan dawo da Sadau.

Masu sukar wannan sanarwa sun nuna mamakinsu kan yadda jarumin Kaduna, wato Rikadawa, ya sa hannu a kan sanarwar da sunan kungiyar jihar Kano, kuma maimakon shugaba ko sakatare su saka hannu kan sanarwar, sai ya zamana Rikadawa ya kira kansa da mataimakin sakatare ne a cikin sanarwar.

Ita kuwa kungiyar furodusoshi masu shirya finafinai sanarwa ta bayar ta na mai bayyana goyon bayanta ga uwar kungiyar a wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta Abba Miko Yakasai da sakatarenta Abdul Amart, inda kuma su ka yi kira ga gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Amir Muhammadu Sanusi II, da su ja kunnen Afakallahu kan wannan batu, sannan su ka nemi Afakan da ya nemi gafarar al’ummar jihar ta Kano.

Masu sukar wannan sanarwa na da ra’ayin cewa, don me kungiyar bangaren furodusoshin ba su fito sun bayar da wata sanarwa ba tun da a ka fara rikicin sai a wannan lokaci da baraka ta kunno kai?

To, ko ma dai mene ne, rahotanni sun tabbatar da cewa, a tsakiyar makon nan a ka yi wani zama tsakanin Afakallahu da shugabannin MOPPAN na kasa (Shugaba Abdullahi Maikano da Babban Sakatare Ahmad S. Alkanawy) a ofishin shugaban hukumar daraktoci na hukumar tace finafinan, inda a ka yi matsayar taka wa Afakallahu birki kan katsandan a al’amuran da su ka shafi hakkin kungiya da ’ya’yanta.

Wannan ne irin sabanin da ya faru a dalilin rikicin da ya balle tsakanin wasu jiga-jigan masu ruwa da tsaki a Kannywood, wato Afakallahu da Officer. Sai mu zura idanu mu ga yadda za ta kaya!

 

 

Exit mobile version