An fitar da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars daga gasar zakaru ta CAF Confederation Cup a ranar Asabar din data wuce bayan ta tashi wasa 0-0 da kungiyar kwallon kafa ta A.S.C Jaraaf ta kasar Senegal.
Pillars, wadda akafi sani da masu Gida sun fice daga gasar ne sakamakon sun kasa rama 3-1 da aka dura musu a Senegal ranar 27 ga Nuwamba sai dai an buga wasan ne a filin wasa na Ahmadu Bello da ke garin Kaduna a yammacin Asabar, inda aka doke ta 3-1 wasa gida da waje.
Ita ma kungiyar Plateau United ta fice daga Gasar Zakarun Afirka ta CAF Champions League bayan ta tashi wasa 0-0 da Simba Sports Club a kasar Tanzania inda itama a wasan farko da suka buga a Najeriya, Plateau United ta sha kashi da 0-1. An doke ta 1-0 a wasa gida da waje kenan.
Ita ma kungiyar kwallon kafa ta Ribers United kashi ta sha a hannun Futuro Kings daci 2-1 a gasar CAF Confederation Cup har gida sai dai kungiyar Enyimba ce kadai ta ci wasanta na farko 1-0 a gasar Zakarun Afirka daga Najeriya, inda ta doke Rahimo FC 1-0 a Najeriya kuma ranar Lahadi suka fafata a wasa na biyu suka tashi 1-1 a birnin Aba na jihar Abia.