Mai bai wa gwamnan Jihar Kano shawara kan harkokin addinai II, Gwani Musa Hamza Falaki ya bayyana cewa tallafin naira biliya biyar da gwamnatin tarayya ta raba wa jihohin domin rage radadin cire tallafin man fetur, sai da gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf y araba fiye da abin da aka bai wa jihar.
Falaki ya bayyana haka ne ga manema labarai a lokacin da yake karin haske kan irin kokarin da gwamna Abba ya yi domin faranta wa Kanawa rai. Ya ce abin da jama’a ba su sani ba shi ne, kudin da aka ce gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi na naira biliyan biyar domin rage wa jama’a radadin cire tallafin man fetur ya yi kadan a Kano duba da yawan al’ummar da take da shi.
Ya ce saboda kaunar talakawa da Gwamna Abba ke ya shiga ya fita ya sake lalubo karin sama da naira miliyon hudu, inda aka karo kayan abinci aka kuma raba wa al’ummar Kano.