Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), ta sanya sabon kwanan watan gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.
Shugaban Hukumar KANSIEC, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne, ya sanar da sauya ranar a wani taron manema labarai a ranar Juma’a.
- Yaushe Tauraruwar Mbappe Za Ta Fara Haskawa A Madrid?
- Kakakin Ma’aiktar Tsaron Sin Ya Gabatar Da Yadda Aka Gudanar Da Atisayen Hadin Gwiwa Na Sojojin Sin Da Tanzaniya Da Mozambique
Leadership Hausa, ta ruwaito cewa da farko dai hukumar ta tsara gudanar da zaben ne a ranar 30 ga watan Nuwamba, amma yanzu za a gudanar da zaben a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.
Ya ce an yanke shawarar rage wa’adin zabe ne domin bin hukuncin kotun koli da ta bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu.
Ya kara da cewa duk shirye-shiryen yakin neman zaben jam’iyyun siyasa zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumba, ta kuma kare a ranar 25 ga watan Oktoba.