Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home MAKALAR YAU

Kanu: Tatsuniya Don Yara

by Tayo Adelaja
September 25, 2017
in MAKALAR YAU
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Ibrahim Sheme    isheme@yahoo.com          +23408036426431

Ina yara? Ga ta ga ta nan ku. A wani gari can cikin kasashen yamma an yi wani hatsabibi wai shi Kanu. Mutum ne wanda ya dauki kan sa a matsayin ya fi kowa sani ko ilimi da kuma kishin kasa. Ya kan bayyanar da hakan a duk lokacin da ya zauna ya na hira da tsararrakin sa ko manyan mutane ko na kasa da shi ko ma bare. To amma duk kishin da ya ke hankoron ya na da shi, ba na dukkan kasa ba ne, na wani bangare ne inda ‘yan kabilar sa su ke. A ganin sa, kabilaar sa mutane ne ne da ke cikin kangin bauta a cikin kasar su ta haihuwa. Ya na ganin ba a kulla komai da su a kasar, an maishe su gugar yasa. Maganin haka kawai, a tunanin sa, shi ne kabilar tasa su ~alle daga kasar, su yi tasu ta kan su, ta ‘yan yaren su kadai da kuma duk wani karamin yare da ke makwabtaka da su. Kuma babu yadda za a cimma nasarar haka sai an zub da jini tunda dai mahunkuntan kasar ba za su yarda da ~allewar ba sai an yi turnuku, an fidda raini. A hangen sa, hanyar lalama ba hanya ba ce mai bullewa.

Kanu ya tabbatar wa da masu sauraren sa cewar tilas ne su tanadi makamai da makudan kudade saboda gagarumin aikin da ke gaban su. Da wannan tunanin Kanu ya ke kwana ya na tashi.

Amma fa ba a banza wannan dan tahaliki ya ke ta wannan hakilon ba; akwai wata a kasa. Ya samu dimbin magoya baya masu ba shi kwarin gwiwa, wasu har da masu-gida-rana. Akwai alamun ma cewar wasu har alkawarin ba shi makamai sun yi domin ya yaki kasar sa saboda a cimma burin ~allewa. Masu bin bahasin maganar sun hango hakan ne tun daga muggan kalaman da ke fitowa daga bakin Kanu. Ban da bayanan karya da gaskiya da ya rika cakudawa ya na yadawa, har ashariya ma ya rika yi, ya na zagin shugabannin kasar da wasu kabilu da ya ce sun yi wa mutanen sa tarnaki hana mika. Hasali ma, shi a wurin sa sunan kasar Gandun Dabbobi. Irin kalaman nasa sun fi yin kama da na wanda ya yi tatil da giyar mulki, ba ya ganin kowa da gashi a ka.

Ganin cewar ya kai bante, sai Kanu ya shiga jirgi, bai zame ko’ina ba sai kasar sa da ke nahiyar Sudaniyya, wato ya bar waccan kasar inda ya je cirani. Zuwan sa ke da wuya kuwa ya daura yaki ba ji ba gani, amma fa yakin cacar baki wanda daga kan sa ne ake komawa na makamai. Ya samu daurin gindin ‘yan ma’abba, ‘yan taratsi, masu amsa-kuwwar kai sako nesa. Kafin ka ce kwabo duk kasar ta dume da kugin kugen Kanu, sai ka ce an yi cida.

To, a dokar kasa, irin wannan yekuwar tare da barazanar kifar da shugabanni karfi da yaji ba ya cikin sharuddan ‘yancin furta ra’ayi, a’a, babban laifi ne wanda hukuncin sa ma kisa ne ko daurin rai da rai. Don haka shugabanni su ka cafke Kanu, su ka kai shi gaban kuliya domin a tabbatar da laifin sa a yi masa hukuncin da ya dace. An yi ta tafka muhawara a gaban kuliya kafin a karshe kuliya ya ba Kanu beli bisa wasu kwararan sharudda.

Da ya kwaci kan sa, maimakon ya nabba’a, ya jira ranar komawa gaban kuliya domin a kare shari’ar nan, sai gogan naka ya yi wancakali da dukkan ka’idojin beli da aka gindaya masa. Su kuma ‘yan kore da magoya bayan sa babu wanda ya tsawata masa, gudun kada a yi masa bi-ta-da-kulli. Kai, wasu dattijan ma caffa su ka kai masa, su na cewa ya isa namiji. Wannan abu ya kara iza wutar kangarewar Kanu, ta inda ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. A majalisun hira babu abin da ya fi daukar hankali kamar zancen Kanu; duk inda ka gitta maganar sa ka ke ji, masu yabo na yi, masu suka na yi, masu tsinuwa ma na yi. Kasa ta rabu gida biyu a kan kadarkon zaman tare ko wargajewa. Su kuma hukumomi sai su ka zura ido tsawon lokaci, ana tunanin sun rasa alkiblar da za su yi kalla, sun rasa abin yi da Kanu. Ya zame masu kadangaren bakin tulu – a kas ka a kas tulu, a bar ka ka bata ruwa!

Shi kuma gogan sai ya rika tunanin lallai an firgita da shi, gidan sa ya zana na dodo, kuma ba ya tabuwa ga kowa. Don haka ya shiga lalata iri-iri a fadar mulkin sa, yau ya takalo wancan, gobe ya tsokano wancan. Ya sauya shiga, ya canza murya, takun tafiyar sa ya zama sabo. Ga wasu, ya zama abin bauta, ana faduwa gaban tafukan kafar sa don neman tubarraki. Har barade nasa na kan sa ya tattara, ya yi runduna, ya ba su kayan sarki da makamai, ya umarce su da kowa ya taba su kada su kyale shi har sai sun ga ba ya motsi. Da yawan magoya bayan sa su ka fara yi masa kallon shugaban kasa a sabuwar daular da ya kafa.

Ashe gaskiyar masu iya magana da su ka ce yaki dan zamba ne! Ashe duk lamon da shugabannin kasar su ka yi ba tsoro ba ne; ja da baya ga rago ne. Kawai jira su ke Kanu ya kai su makura su sauko su fyade shi. Ai kuwa hakan aka yi.

Ta’asar Kanu ta kai intaha ne lokacin da wasu ‘yan kabilar sa su ka fara kai hari ga kabilun yankin arewa na kasar, musamman wadanda ya ke ganin daga cikin su ne shugaban kasa ya fito. Kuma fa abin duk siyasa ce ta kabilanci wadda ta yi wa kasar katutu. An gaje ta tun zamanin ‘yan mulkin mallaka. Ta ki gushewa. Abin ya kai komai sai an sa gilashin kabilanci ko addini ake kallon sa. Don haka hare-haren da jama’ar Kanu su ka fara kaiwa duk saboda kabilancin ne, amma sai aka boye da guzuma ana harbin karsana, ana wasu wawuke-wawuke marasa kangado. Kuma an manta da tarihi. An manta da cewa irin wadannan wawuke-wawuken ne su ka jawo hatsaniyar da ta kai ga muggan kashe-kashe a shekaru hamsin baya, ciki har da yakin basasa na tsawon wata talatin. Amma da yake su su Kanu su na cikin cikin iyayen su ko su na ‘yan jarirai aka yi wancan rikicin, sai su ke dabi’a kamar ba su san an yi ba, kamar ba su karanta a littattafan tarihi ba.

Shugabanni sun yanke shawarar yi wa tufka hanci ne lokacin da su ka ga izgilancin Kanu ya kai magaryar tukewa, musamman da aka fara kashe-kashe kamar yadda dan tawayen ke so. Nan da nan aka zaburi dakarai masu fushi da fushin wani, aka cinna wa Kanu su. Haba! Kan ka ce kwabo an murkushe tawayen Kanu, an tuna wa mabiyan sa cewa Barno fa gabas ta ke. Yanzu ko ‘ihn’ din su ba ka ji!

Shin tatsuniyar ta kare kenan? Wallahi a’a. Da sauran rina jingim a kaba. An dai kashe maciji, amma ba a sare kan ba. Kanu fa ba shi kadai ba ne; ya na da masu dafa masa baya fai da boye. An ma gano cewa wasu kasashen yammaci ne mafakar magoya bayan sa. A can ne ya ke samo taro da sisin da ya ke amfani da su wajen tada fitina. Kuma a cikin gida ma, ya na da manyan iyayen gida da kuma gwanayen tada kura. Akwai su a ko’ina. Kudirin wargaza kasar ba karami ba ne. Babbar kwangila ce. Ita kwangila a duk inda ake yin ta to akwai ribar ta ga wadanda ke aiwatar da ita. Wato kenan tsugune ba ta kare ba, an saida kare an sai biri!

Babban kalubale shi ne yadda za a magance irin tashin-tashinar da Kanu ya jawo. Akwai kasashen da ke son kasar ta wargaje, a karya alkadarin ta, a yi wasoson dimbin albarkatun da ke cikin ta. Wasu sun ce maganin abin shi ne a sake fasalin kasar; a dauke karfin mulki da ke fadar shugaban kasa, a mika shi ga yankunan kasa ta yadda kowane yanki zai ci gashin kan sa a wasu sha’anoni. Amma kuma wasu sun ce a bar kasa yadda ta ke. Kaka kara kaka?

Ko ma dai menene, tilas a san yadda za a fidda jaki daga duma. Cin kashin ya isa haka.

Yara, bari mu dakata a nan don ku samu ku huta. Amma ku sa ido, tatsuniyar ba ta kare ba. Don haka ba zan ce kurunkus kan dan kusu ba har sai na ba ku karashen tatsuniyar. Mu kwana lafiya, yaran kirki!

SendShareTweetShare
Previous Post

Na Ji Haushin Tafiyar Gibbs Sama Da Ta Chamberlain -WENGER

Next Post

Cikin Wata Guda Mutum 423 Suka Mutu A Hadari –Hukumar FRSC

RelatedPosts

NECO

Kin Biyan Kudin NECO Daliban Katsina Na fuskantar Barazanar Rasa Guraban Karatu  

by Muhammad
7 days ago
0

Tare Da El-Zaharadeen Umar, Katsina 08062212010: Babu shakka babu wanda...

Siyasa

Tsokacin Kolawale (IV) Game Da Alakar ‘Yan Siyasa Da Miyagu

by Muhammad
1 week ago
0

Ci gaba daga jaridarmu ta Juma’ar da ta gabata Dan-jarida...

Al’ada Da Irin Kutsen Da Ake Yi Mata

Al’ada Da Irin Kutsen Da Ake Yi Mata

by Muhammad
1 week ago
0

Kusan dukkan dabi’un mutane, daga zuwa kasuwa, halartar daurin aure,...

Next Post

Cikin Wata Guda Mutum 423 Suka Mutu A Hadari –Hukumar FRSC

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version